Rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna ta sanar cewa an yi garkuwa da mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kaduna Shu’aibu Idris-Lauge da ‘yar sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige ya bayyana haka da yake hira da Kamfanin Dillance Labaran Najeriya a Kaduna.
Jalinge, ya ce an sace Lauge da ‘Yar sa a gidan sa dake Kwanar Zango, Titin Kaduna -Zaria.
Jalinge ya kara da cewa tuni sun fantsama farautar wadanda suka sace Lauge da ‘yar sa da kuma ceto sa daga hannu masu garkuwan.
Discussion about this post