Ina cike da farin cikin warkewar Sarkin Daura daga Coronavirus – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana jindadin sa bisa ga sauki da sarkin Daura, maimartaba Umar Umar ya samu bayan fama da yayi da cutar Coronavirus.

Sarkin Daura maimartaba Umar Umar ya kwanta rashin lafiya a dalilin kamuwa da yayi da cutar Coronavirus. Ya shafe kwanaki 10 a asibitin Gwamnatin Tarayya dake Katsina in da ake duba shi.

Buhari ya ce wannan abin farin ciki ne matuka ga shi da mutanen kasar Daura, da jihar Katsina baki daya.

” A wannan yanayi da muke cika, na fada cikin matsanancin damuwa matuka tun lokacin da aka kwantar da kai. Amma yanzu hankali ya kwanta, na yi farin ciki matuka da na samu labarin ka warke.” In ji Buhari.

A karshe Buhari ya jinjina wa likitocin da suka kula da maimartaba, cewa Najeriya na Alfahari su matuka.

Share.

game da Author