Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 193 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Alhamis, Jihar Legas ta samu karin mutum 58, 46-Kano, 35-Jigawa, 12-Yobe, 9-FCT, 7-Ogun, 5-Plateau
5-Gombe, 4-Imo, 3-Edo, 3-Kwara, 3-Borno, 1-Bauchi, 1-Nasarawa, 1-Ondo.
Yanzu mutum 5162 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1180 sun warke, 167 sun mutu.
Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammadu Badaru ya koka kan yadda cutar Korona ke ci gaba da yaduwa a jihar Kamar wutan daji.
Gwamna Badaru ya ce jihar za ta iya samun sama da mutum 20,000 da za su kamu da cutar, ganin yadda take dada yaduwa babu kakkautawa a ko-ina a fadin jihar.
” Yanzu ya tabbata cewa cutar Korona ta samu gindin zama jihar Jigawa, domin ta yadu zuwa duka kananan hukumomi 27 dake jihar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 184 da suka kamu da cutar ranar Laraba. Jihar Jigawa ta samu karin mutum 23 da suka kamu da cutar.
A jawabin da yayi a taron manema labarai, gwamna Badaru ya ce masana sun kintata cewa za a iya samun mutum 20,000 da zasu kamu da jutar a jihar.
Rashin saka dokar hana walwala da tarukka a jihar Jigawa na daga cikin manyan dalilan da ya sa mutane ke ganin ya sa cutar ke ci gaba da yaduwa a jihar.
Gwamnatin Jigawa bata saka doka kowacce iri bace domin dakile yaduwar cutar.
Bayan haka gwamna Badaru ya ce gwamnati za ta inganta alawus din ma’aikatan lafiya na jihar sannan kuma da saka su cikin shirin inshora.