Sallar sai ranar Lahadi – Inji Sarkin Musulmi, Abubakar

0

Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad ya sanar cewa ba a ga watan Shawwal a Najeriya ba ranar juma’a. A dalilin haka ya yi kira ga daukacin musulmai su ci gaba da Azumin Ramadana ranar Asabar.

Idan aka yi azumi ranar Asabar, an yi 30 kenan, ranar Lahadi kuma sai a tashi da shagulgulan sallah.

Musulmi a Najeriya da sauran kasashen duniya sun yi azumi a cikin lalurar dokar zaman gida dole, saboda annobar cutar Coronavirus da ta barke a duniya.

A kasashe da dama ba a gudanar da sallolin tarawy a masallatai ba. Haka a ranar sallah ma Saudiya ta sanar cewa ba za a yi taron Sallar Idi ba, sai dai kowa a yi idi a gida.

Kungiyar Jama’atu karkashin Shugabancin sarkin musulmi Abubakar, ta yi kira ga mutane su hakura su yi sallar Idin su a gida dimin kiyaye wa daga kamiwa da annobar Korona.

Shugaba Muhammadu Buhari ma ya ce zai yi Sallah ne tare da iyalan sa a gida.

Share.

game da Author