COVID-19: An sallami mutum 13 a Legas

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta bayyana cewa ta sallami mutum 13 da suka warke daga cutar coronavirus.

Cikin su akwai mata 4 da maza 9, kuma duk an sallame su ne ranar Alhamis.

An sallami wadannan mutane ne bayan an yi musu gwajin cutar sau daya a maimakon sau biyu kamar yadda aka saba yi.

A yanzu dai mutum 662 ne aka sallama a jihar Legas.

Mutum 7016 ne suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1907 sun warke, 211 sun mutu.

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce nan gaba za a fara yi wa wadanda suka warke gwajin cutar sau daya a maimakon sau biyu da aka saba yi.

Ma’aikatar kiwon lafiya bayyana cewa duka wanda ya warke kuma aka yi masa gwaji da farko sakamakon zai nuna baya dauke da cutar sannan koda an sake yi hakan dai zai sake nunawa.

Ya ce da a daddage ana yi wa wanda ya warke gwaji har sai biyu gwara arika yin gwajin sau daya kawai a sallami mutum tunda dama can sakamakon gwajin kan nuna hakan ne idan an sake yin na biyun.

Ihekweazu ya ce yin haka zai rage yawan cinkoson mutane sannan da karancin gadajen da ake fama da su a asibitocin kasar nan.

Share.

game da Author