Bayan samun rahoton sake bayyanar cutar Covid-19 a Wuhan, kasar Chana, gwamnatin kasar ta yi wa mutane miliyan 11 gwajin cutar a cikin kwana 10 dake zaune a garin Wuhan.
Gwamnati ta kuma umurci duk unguwannin dake Wuhan su tsara hanyoyin da za su yi wa duk mutanen unguwar su gwajin cutar a cikin kwanaki 10.
Sakamakon gwajin da akayi ya nuna mutum shaidasun kamu da cutar a Wuhan.
An gano wadannan mutane da cutar ta sake kamawa bayan gwamnati ta dakatar da dokar zaman gida dole da ta saka tun a tsakiyar watan Fabrairu zuwa Afrilu.
Mutum sama da 82,000 ne suka kamu da cutar. Daga cikin sama da 4,000 sun mutu a kasar.
Yi wa mutane gwajin cutar, yin feshi a duk wuraren da mutane ke taruwa, kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar, saka dokar zaman gida dole na daga cikin matakan da suka taimaka wa kasar dakile yaduwar cutar.
Gwamnati ta ce wannan karon za ta mai da hankali wajen kare kiwon lafiyar tsofaffi da bangarorin kasar da mutane suka fi yawa domin dakile yaduwar cutar.
Wasu likitoci sunce ganganci ne matakin yi wa mutum milliyan 11 gwajin cutar a cikin kwanaki 10 da gwamnati ta yi a kasar.
Tarihin Covid-19
Cutar Covid-19 ya fara bayyana ne a Wuhan dake kasar Chana a watan Disemba 2019.
A lokacin likitoci sun bayyana cewa su na samun mutane da dama dake fama da wani cuta dake kama da mura a asibitoci.
Bayan haka ne cutar ta yadu zuwa Lardin Hubei kuma ta ci gaba da yaduwa har ta zama annoba a duniya.
Bincike ya nuna cewa cutar ta fara bayyana ne a kasuwar saida kifi da naman ruwa mai suna ‘Huanan seafood’ a garin Wuhan.
Kafin cutar ta zama annoba likitoci sun ce ana kamuwa da cutar a dalilin yawan cudanya da dabobi.
Wadannan dabbobi sun hada da kare,mage,bera, jemage da sauran su.
Daga nan kuma likitocin sun kuma gano cewa ana iya kamuwa da cutar a jikin mutum dake dauke da cutar.