Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 245 da suka kamu sannan mutum 10 sun mutu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Juma’a.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Juma’a, Jihar Legas ta samu karin mutum 131, Jigawa – 16, Ogun – 13, Borno – 12, Kaduna – 9, Oyo – 9, Rivers – 9, Ebonyi – 9, Kano – 8, Kwara – 7, Katsina – 5, Akwa Ibom – 3, Sokoto – 3, Bauchi – 2, Yobe – 2, Anambra – 1, Gombe – 1, Niger – 1, Ondo – 1, Plateau – 1 FCT – 1, Bayelsa – 1.
Yanzu mutum 7261 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 2007 sun warke, 221 sun mutu.
Hukumar NCDC ta ce ta yi wa mutum 41,907 gwajin cutar inda sakamakon gwajin ya nuna cewa 7261 na dauke da cutar.
Daga ciki mutum 5,033 na kwance a asibiti, an sallami 2,007 sannan 221 sun mutu.
Gwamnatin Tarayya ta roki Gwamnonin da ke dage dokar hana walwala saboda Coronavirus, su canja tunani, domin hakan kan iya sake barkewar cutar fiye da kima a cikin al’umma.
Duk da karin yawan masu cutar Coronavirus da ake samu a kasar nan, wasu jihohi sun janye dokar hana walwalar jama’a .
Daga cikin jihohin da suka janye dokar akwai Bauchi, Kano, Adamawa, Cross Ribas, Barno, Ebonyi da sauran su.
Jihohin sun amince jama’a su rika cin kasuwa, zuwa masallatai da coci-coci.
Sakataren gwamnatin tarayya da shine shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar Korona a Najeriya, Boss Mustapha ya ce akwai barazana ga jihohin da aka bude yanzu ana al’amurra, duk kuwa da cewa cutar na kara yaduwa a yanzu a nan Najeriya.
Ya ce ya kamata a guji duk wani taro da ya kai na akalla mutum 20 abin da ya yi sama.