Eid-el-Fitr: A ci gaba da hakuri dai – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon barka da sallah ga dukkan musulman Najeria.

A sakon taya murnar Kammala azumin ramadana da bukin sallar Eid-El-Fitr, shugaba Buhari ya yabawa ‘yan Najeriya kan bin doka da suka yi a wannan lokaci da duk duniya ake fama da annobar Korona.

” An yi azumin bana cikin wani yanayi da ba a taba ba. Mutane sun saba gudanar da ayyukan ibada da dama a lokacin Azumi, amma hakan bai yiwuwa mutane ba a bana saboda halin da duniya ta fada ciki na annobar Korona.

” Ba a samu an halarci wuraren tafsirin Kur’ani ba, ba a yi sallolin jam’i da taraweeh ba da kuma tafiya Umra da akan yi a lokacin Azumi.

Buhari ya ce ya na sani da matsalolin da mutane suka shiga da takura da suka yi fama da a dalilin dokokin da aka sassaka don dakile yaduwar Korona a Najeriya.

” Babu gwamnatin da za ta saka mutanen ta cikin kangi haka kawai da gangar. A ci gaba da hakuri sannan kuma gwamnati zata rika duba yanayin yaduwar cutar domin sassauta dokoki akai akai.

Haka kuma Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai yi sallar Idi da Iyalan sa a gida sannan ya hori jama’a suyi Idi a gida domin kauce wa gwamatsuwa da mutane idan aka ce za ayi gangami a tafi idi a waje.

Haka shima Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi sallolin idin su a gidajen su.

Share.

game da Author