KANO: Ganduje bai kyauta mana ba zaftare albashi da yayi – Ma’aikatan Kano

0

Ma’aiktan jihar Kano sun kwana nuku-nuku tun daga ranar Alhamis da gwamnati ta biya su albashin watan Mayu.

Da yawa da suka zanta da PREMIUM TIMES sun shaida cewa gwamnati bata kyauta musu ba zaftare musu albashi da tayi.

” Ni dai kusan naira 20,000 aka cire min a albashina. Gaba daya ya dagula min lissafin da nayi na shirin Sallah. Wannan abu bai yiba.” Inji ma’aikaci

Ma’aikata sun ce gwamnati ta yanke musu albashi ba tare da sanar dasu su kwana da shiri ba. ” Kawai sai ka je cire kudi sai ATM ta yi maka kararrawa, cewa kudin ka bai kai ba.

Wasu sun ce gwamnati ya yanke karin da tayi wa ma’aikata ne da ta daga karancin Albashi daga 18,000 zuwa 30,000 sai ta maida albashir yadda yake ada.

Idan ba a manta ba a farkon wannan mako, gwamnan Abdullahi Ganduje ya rage albashin ‘yan siyasa da aka nada mukamai a jihar da kashi 50 bisa 100.

Sakataren yada labaran gwamnatin jihar Kano, Awwal Anwar ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Kano.

Anwar ya ce hakan ya biyo bayan karyewar tattalin arziki ne da aka samu da karancin kudaden shiga a dalilin annobar Korona.

” Saboda rashin samun isassun kudaden shiga yanzu a dalilin annobar Korona duka ‘yan siyasa da aka nada za su rika amsar rabin alabshin su ne daga watan Mayu. Hakan ya hada harda gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da mataimakin sa Nasir Gawuna.

” A dalilin Annobar Korona, da garkame gari da aka yi, kusan duka kamfanonin dake Kano basu aiki. hakan yasa ana samun karancin kudaden shiga.

Ganduje yace wannan rage albashi da gwamnati ta yi ya hada harda shugabannin kananan hukumomi da mataimakan su, kansiloli, masu bada shawara da dai duk wanda siyasa ce ta nada shi.

Share.

game da Author