• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

    Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

    Nigerian Pilgrims

    HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

    Beggars

    Almajirai da mabarata sun kwararo Abuja – Mahukunta

    HARƘALLAR KWANGILA: EFCC ta kama Patricia Etteh, tsohuwar Kakakin Majalisar Tarayya

    Ƴan bindiga sun ƙona hedikwatar karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra

    UMARNIN SALLAMA DA KUJERAR MINISTA: Pauline Tallen, Timiprr Sylva duk sun janye daga takara

    Na koma PDP ne don in kawo karshen mulkin kama karyar da APC ke yi a Jigawa – Saminu Turaki

    Gumi yayi kakkausar jan kunne ga waɗanda suka kashe Deborah, ya ce ba hurumin su bane yanke hukuncin kisa don an zagi Annabi SAW

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

DOKAR CUTUTTUKA: Majalisar Tarayya ta maida wa Tambuwal da Gwamnonin Najeriya martani

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
May 15, 2020
in Manyan Labarai
0
DOKAR CUTUTTUKA: Majalisar Tarayya ta maida wa Tambuwal da Gwamnonin Najeriya martani

Gbajabiamila Femi

Majalisar Tarayya ta maida wa Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto kakkausan martani, dangane da matsayar da Gwamnonin Najeriya suka dauka, cewa a jingine Kudirin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a cikin jama’a, bisa dalilin cewa Majalisar Tarayya ba ta tuntubi gwamnonin ba.

Kudirin dokar dai Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya kirkiro shi.

Cikin wata takardar kakkausan raddi da Majalisa ta maida wa Tambuwal, wanda ya sa wa takardar gwamnoni hannu, a madadin sauran gwamnonin, Kakakin Yada Labaran Majalisa, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa bai ga dalilin shisshigin gwamnoni na rubuto takardar ba, domin tuni majalisa ta jingine kudirin, ta ce za a ji ra’ayoyin jama’a tukunna.

Tambuwal nukura ya ke wa Gbajabiamila -Ben Kalu

Benjamin Kalu ya ce ba wani abu ya sa Gwamna Tambuwal ke ta sagarabtu a kan kudirin ba, sai nukura kadai da ya ke wa Shugabancin Majalisar Tarayya, a karkashin Femi Gbajabiamila.

Kalu ya kara da cewa Tambuwal ya lura Majalisa a yanzu sai kara samun tagomashi ta ke yi, sabanin lokacin da ya yi shugabancin ta, da kuma bayan saukar sa, tsakanin 2015 zuwa 2019.

“Tambuwal ya sani sarai a matsayin sa na gogaggen tsohon dan majalisar tarayya, wanda har shugabancin majalisa ya rike, kudiri iri-iri ne.

“Akwai kudirin da ba ya bukatar sai an kai wa Majalisar Dokokin Jihohi ko Gwamnoni kafin a amince da shi ya zama doka.

A cire Tambuwal daga cikin kwamitin Tattaunawa Da Majalisa

“Mun Amince cewa gwamnoni abokan tafiyar Majalisar Tarayya ne wajen ciyar da kasar nan gaba. To amma fa ya kamata su sani cewa mu ba ‘yan-amshin-Shatan su ba ne, kuma ba a karkashin gwamnoni mu ke ba. Sai fa idan a yanzu so su ke yi a sauya doka mu koma karkashin su.

“Ba mu yadda da Gwamna Tambuwal a cikin sunayen gwamnoni uku da za su yi zaman tattaunawa da shugabannin majalisa ba. Domin tuni ya nuna son rai a cikin lamarin. Kasancewar sa tsohon Shugaban Majalisar Tayyaya, zai iya yin kane-kane, ya hana sauran bakin magana.”

Waiwaye: Yadda Tambuwal Ya Fusata Shugabannin Majalisar Tarayya

Ranar Alhamis PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin taron-dangin da daukacin Gwamnonin Najeriya 36, su ka yi wa Majalisar Tarayya, inda su ka ce sun ki amincewa da Kudirin Dokar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa, wadda yanzu haka ake tafka kwatagwangwamar hayaniya saboda ita a Majalisar Tarayya.

Kudirin dokar mai suna ‘Control of Infectious Diseases Bill’, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne ya gabatar da shi a Majalisa.

Duk da cewa bai samu na’am da karbuwa daga masu yawan mambobin majalisar ba, tuni kudorin har an yi masa karatu na biyu a zauren majalisa, kafin korafe-korafe, suka, caccaka su sa a dakatar da batun sa.

Yadda Kudirin Dokar ya yi bakin jini

Kafin Gwamnonin Najeriya su nuna rashin amincewa da kudirin, ‘yan Najeriya da dama da wasu ‘yan Majalisa duk sun nuna damuwa dangane da yadda ake ta gaggawa, azarbabi da rawar jikin hanzarta amincewa da kudirin.

Ana ta mamakin yadda a ranar da aka gabatar da kudirin yadda Shugaban Majalisa, Femi Gbajabiamila ya hakikice wajen amimcewa da kudirin, duk kuwa da cewa kusan gaba dayan ‘yan majalisar ko samun damar lokacin karanta kudirin mai babi 82 ba su yi ba.

Wannan kurman karatu da Gbajabiamila ya biya wa mambobi, ya haifar da rashin amimcewa daga ‘yan Najeriya masu bibiyar al’amurran yau da kullum.

Kudiri Ko Satar-fasaha?

An rika yin tir da cewa gaba dayan kudirin wankiya aka yi daga wata dokar kasar Singapore, wadda kasar ke amfani da ita wajen kokarin dalile cututtuka masu yaduwa.

Salon rubutu, Turancin da aka yi amfani da shi da kalmomin da ke cikin kudirin mai babi 82, an tabbatar da cewa duk satar-fasaha ce aka kwafo daga dokar Singapore.

Kungiyoyin kare hakkin jama’a kuma sun rika yin kururuwar cewa kudirin idan ya zama doka, to za ta takura kuma ta danne hakki tare da tirsasa wa ‘yan Najeriya yin abin da bai dace a tirsasi a karkashin mulkin dimokradiyya ba.

An kuma yi korafi a kan wani babi, wanda zai tilasta kowane mai fita kasashen waje da mai shigowa sai ya mallaki katin shaidar lafiyar sa garau. Wannan wani kati daban aka bijiro da shi a cikin kudirin, wanda ba ‘yelo card’ da matafiya suka sani ana amfani da shi ba.

Ba Mu Yarda Da Kudirin Ya Zama Doka Ba -Gwamnonin Najeriya

Cikin takardar da Mataimakin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Aminu Tambuwal, Gwamnan Sokoto ya sa wa hannu, gwamonin su 36, sun ce sun ki amincewa da kudirin domin ba a tuntube su ba, a matsayin su na jagororin jama’ar da ake kokarin a kakaba wa dokar.

Sun kara da cewa ya kamata a nemi jin ra’ayin jama’a kafin a yi azarbabin yanke hukuncin neman a mayar da kudirin zuwa doka.

Sannan kuma Gwamnonin sun karta alamar tambaya dangane da karfin ikon tirsasa killace mutum da kuma tilasta yi masa allurar rigakafi da kudirin dokar ya bai wa Ministan Lafiya da Shugaban Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).

Gwamnonin sun ce tilas majalisa ta jingine kudirin. Sannan kuma sun nada gwamnonin Sokoto, Katsina da Filato su zauna su yi nazarin kudirin daga nan su zauna da shugabannin Majalisar Tarayya domin a sake tsefe gashin kan kudirin dokar gaba daya, ba don komai ba, suka ce don kada a yi wa ‘yan Najeriya kitso da kwarkwata.

Tags: Abuja NajeriyaDokaFemiHausaLabaraiMajalisaTambuwal
Previous Post

Karakainar da ake yi duk da dokar hana tafiye-tafiye a jihohi, ta sa shakku a kan tsaron Najeriya

Next Post

Yadda Kudirin Dokar Cututtuka ya yi bakin jini

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • FASHEWAR TUKUNYAR GAS A KANO: Ministar Jinƙai na so a ɗau matakan hana aukuwar bala’o’i
  • Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80
  • Hukumar NAPTIP ta cafke matar da ta shahara wajen ciniki da safarar mutane
  • KADUNA TA DAGULE: Boko Haram sun darkako Kaduna, ta’ammali da muggan kwayoyi ya yi tsanani a jihar – El-Rufai
  • 2023: APC ta canja ranakun zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.