Karakainar da ake yi duk da dokar hana tafiye-tafiye a jihohi, ta sa shakku a kan tsaron Najeriya

0

‘Yan Najeriya sun damu kwarai da yadda a kullum su ke karanta labarai da ganin bidiyon dimbin matafiyan da ake kamawa, masu baro jihohin su zuwa wasu, duk kuwa da cewa akwai dokar hana tafiye-tafiye.

An dai kakaba dokar hana tafiye-tafiye saboda a hana yaduwar cutar Coronavirus a cikin kasa.

Matafiyan sai akasari ana jigilar su ne a cikin manyan motoci masu dauke da abinci ko dabbobi. Wannan zirga-zirga kuwa koma-baya ce ga kokarin da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ke yi wajen hana Coronavirus fantsama.

An ganin cewa matsawar jama’a na karakaina, daga inda babu ita zuwa inda ke da ita, ko kuma daga inda ke da ita zuwa inda babu ita, to cutar za ta ci gaba da fantsama a cikin jama’a, kamar wutar-daji.

Babu Kwakkwaran Tsaro A Najeriya

Wannan matsala ta karakainar matafiya a lokacin dokar hana tafiye-tafiye, ta nuna karara yadda harkar tsaro ta sakwarkwace a kasar nan.

A kan haka ne Majalisar Dattawa a ranar Talata, ta nuna fushin ta, tare da zartas da matsaya cewa Sufeto Janar na Najeriya ta sa a binciki dukkan jami’an tsaron da ake zargin ana hada baki da su, matafiya da direbobi na ba su kudi su na wucewa zuwa garuruwan da suka dosa.

“Hukumar NCDC ta nuna damuwa a kan yadda ake jigilar matafiya, daga wannan jiha zuwa waccan, a lokacin da hukumar ke kokarin dakile cutar Coronavirus.

” Gwamnoni su ma sun nuna damuwa a kan yadda ake lodin jama’a a cikin motocin daukar abinci da dabbobi ana wucewa wasu jihohi da su, duk kuwa da dokar hana tafiye-tafiye da aka yi.”

Furucin Sanata Ike Ekweremadu kenan, wanda shi ne ya gabatar sa korafin a zauren Majalisar Dattawa.

Ya ci gaba da nuna yadda jami’an tsaro ke bari ana fatali da dokar shugaban kasa, ta hana zirga-zirga, tare da nuna yadda ake zargin jami’an ‘yan sanda na cuwa-cuwar karbar kudi a hannun direbobi da fasinjoji su na wuce shingayen jami’an tsaro.

Jihohi irin su Rivers, Akwa Ibom, Abia, Bayelsa da Ondo duk sun karkata lodin ‘yan Arewa ‘yan ci-rani da suka yi kokarin shiga jihohin a lokacin da ake cikin dokar hana tafiye-tafiye.

A Abuja babban birnin Tarayya, a kullum dimbin motoci na shiga da lodin fasinjoji daga jihohi da garuruwan da ke makwautaka da birnin.

Yayin da ake ci gaba da sukar jami’an ‘yan sanda, Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba, ya ce a rika yi wa jami’an su adalci.

Ya ce da yawan matafiya shigar-burtu suke yi, ko su yi shigar jami’an lafiya, ko su ce ‘yan jarida ne.

Ya ce ayyukan na yi wa jami’an su yawa. Saboda haka ba kamar jami’an kwastan ba ne, wadanda ke tsayawa kan iyaka, su kama bakon-haure.

Ya ce masu shiga Abuja daga wasu jihohin na biyowa ta barauniyar hanya ce.

Share.

game da Author