Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa mai Dalike Cutar Coronavirus, Boss Mustapha, ya bayyana dalilan da suka sa Shugaba Muhammadu Buhari ya kara tsawon dokar hana tafiye-tafiye tsakanin jihohi da ta zirga-zirgar dare a kasar nan.
Da ya ke jawabi wurin taron manema labarai a ranar Litinin, Mustapha ya ce tilas ce ta sa kwamitin sa ya bai wa Buhari wannan shawara, kuma ya amince da ita.
Lokacin Bude Hada-hada A Kasa Baki Daya Bai Yi Ba: Boss Mustapha ya ce sun shaida Buhari cewa lokacin sakin kowa da kowa ya ci gaba da harkokin yadda aka saba a da, bai yi ba tukunna.
Ya ce duk da an samu ci gaba a wajen kokarin dakile cutar, lokacin bude dukkan harkoki baki daya a kasar nan bai yi ba. Don haka akwai bukatar kara makonni biyu tukunna.
Don Amfanar Jama’a Ne Aka Kara Makonni Biyu: Boss Mustapha ya ce jama’a su kara hakuri da juriya, domin tsawaitawar ba za ta yi musu dadi ba. Duk da haka, ya za a ma kara tsaurara dokar domin tabbatar da cewa an samu gagarimar nasarar da kowa zai amfana, idan aka dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin kasar nan.
Idan Aka Saki Kowa A Yanzu Za A ‘Ballo Ruwa’: Mustapha ya ce sun auna sun hango yadda al’amurra ke tafiya a yanzu a inda ake samun nasarori da kuma inda ake samun cikar.
“Saboda haka idan aka saki kowa aka ce duk kasar nan kowa ya fito a ci gaba da harkoki baki daya, to akwai barazanar maida hannun agogo baya.
“Amma cikin makonnin nan biyu masu zuwa, za mu zage damtse wajen magance kananan matsalolin da ake fuskanta a wasu wurare ko jihohi da sauran su.”
Don A Bai Wa Kowane Bangaren Harkokin Hada-hada Damar Shiryawa Tsaf Kafin Makonni Biyu: Wannan dalilin ne ya ce, idan aka saki kowa a yanzu, to bangarori da dama ba su shirya wa kokawa ba. Saboda haka idan ma an koma din, to al’amurra za su rika yin tafiyar-hawainiya da kwan-gaba-kwan-baya.
Don Mu Kara Kaimin Zakulo Masu Cuta Da Kula Da Wadanda Ke Killace: Shugaban Kwamitin Dakile Coronavirus ya ce wa’adin makonni biyu da Buhari ya kara zai kara wa kwamitin sa kaimin tashi tsaye ya na zakulo masu cuta, ana gwaji kuma ana ci gaba da kula da wadanda aka killace.
Wannan dokar zai ta tafa aiki ne daga Litinin da dare, 18 Ga Mayu zuwa 1 Ga Yuni.