Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Kasa (NSCIA), ta fitar da sanarwar fara duba sabon watan Shawwal a ranar Juma’a, 22 Ga Mayu.
Cikin watan sanarwa da Mataimakin Sakataren Majalisa, Salisu Shehu ya sa wa hannu, ya ce ranar 22 Ga Mayu, wato Juma’a mai zuwa ce daidai da ranar 29 Ga Ramadan.
“Saboda haka sakamakon shawara da nazari, ana sanar da daukacin musulman kasar nan su fara duban sabon watan 1 Ga Shawwal, a ranar Juma’a da yamma.
“Hukumar Lura da Sararin Samaniya ta Kasa ta ce watan zai iya ftowa kafin ranar ta fadi a ranar Juma’a. To amma ba zai dade ba, cikin kankanen lokaci zai dusashe.
“Saboda haka mu na sanar da jama’a cewa bayan sallar Magriba a ranar Juma’a din, idan rana ta fadi za a iya katarin ganin watan, duk da ba a iya ganin sa kafin faduwar rana ba.”
Sanarwar da Majalisar ta fitar, wadda Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ne shugaban ta, an yi wa daukacin musulmi fatan alherin kammala azumi lafiya tare da neman lada da albarkacin da ke cikin qata Ramadan.
Sannan kuma an yi addu’a da fatan Allah ya sa mu ga azumin shekarar Musulunci ta 1442 mai zuwa.
Musulmi a Najeriya da sauran kasashen duniya sun yi azumi a cikin lalurar dokar zaman gida dole, saboda annobar cutar Coronavirus da ta barke a duniya.
A kasashe da dama ba a gudanar da sallolin tarawy a masallatai ba. Haka a ranar sallah ma Saudiya ta sanar cewa ba za a yi taron Sallar Idi ba, sai dai kowa a yi idi a gida.
Discussion about this post