Canja ranakun cin Kasuwa a Kaduna: Gwamnati ba za ta lamunta wa masu baje kayan siyarwa a gefen Kasuwannin da aka garkame ba

0

Gwamnatin Kaduna ta canja ranakun zirga-zirgar jama’a daga ranakun Labara da Asabar zuwa ranakun Laraba da Alhamis.

Shugaban hukumar kula da kasuwannnin jihar Hafiz Bayero ne ya sanar da haka kamar yadda kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ta ruwaito.

Bayero ya ce babu wata kasuwa da za ta ci ranar Asabar, kowa ya yi cefanen sa ranar Laraba da Alhamis kuma a sabbin kasuwanni firamare da gwamnati ta amince da su a fadin jihar.

Bayan haka Bayero ya gargadi masu cin kasuwa a gefen kasuwannin da ak garkame da su shiga taitayin su. Gwamnati ba za ta lamunta wa duk wanda yake baje kayan sana’ar sa ko kuma ya bude shago a kasuwannin da aka garkame ba.

Duk mai bukatar siyan abinci ya garzaya firamare ya siya.

” Za a bude kasuwannin firamare daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma. Sannan kuma a kiyaye saka takunkumin fuska da yin nesa-nesa da juna.

Share.

game da Author