Kodinaton yada labaran rundunar sojin Najeriya John Enenche ya bayyana cewa zaratan sojojin Najeriya sun aika da Boko Haram 20 lahira a arangaramar da suka yi a garin Baga, jihar Barno.
Enenche ya shaida cewa Boko haram din basu sha da dadi ba domin baya ga kashe su da sojoji suka yi suk kwato manyan makamai daga wurin su.
Sai dai kuma ya ce wasu sojoji 9 sun samu rauni a wannan arangama da yanzu haka suna asibiti ana kula da su.
Yace babu soja ko daya da aka rasa a wannan arangama da suka yi da Boko Haram.
Discussion about this post