Mataimakin Gwamnan Jihar Barno ya bayyana cewa halayyar bijire wa sharudda da ka’idojin kauce wa kamuwa da Coronavirus da mutane ke nuna wa, daidai ta ke da irin yadda aka rika bijire wa doka har aka wayi gari Boko Haram ya kunno kai a jihar.
Umar Kadafur, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus na Jihar Barno, ya yi wannan furucin a cikin halin damuwar ganin yadda al’ummar Jihar Barno ke bijire wa doka da ka’idojin kauce wa cutar da aka gindaya, musamman umarnin su daina gwamutsuwa da cunkushewa a wuri daya.
Da ya ke bayani a gaban manema labarai, Kadafur ya ce duk da wannan halayyar da jama’a ke nunawa, guiwar su ba za ta yi sanyi ba, za su gaba da aikin da suka sa gaba na dakile cutar Coronavirus, saboda cutar gaskiya ce, akwai ta.
“Kun dai gani da idon ku yadda a ranar Asabar jama’a suka bijire wa umarnin kaffa-kaffa da shiga tirmitsitsi da cinkoson jama’a, suka yi dandazo da tururuwa wajen tafiya rufe gawa. Saboda kawai tunanin su ya raya musu cewa Coronavirus karya ce.” Inji Kadafur.
Mataimakin Gwamna ya na bada misali ne da yadda mutane suka cika makil wajen jana’izar wani babban malamin Musulunci, Modu Goni Kolo, wanda ya rasu ranar Asabar, inda dandazon daruruwan mutane suka rika gugumarar da turereniyar kokarin taba gawar malamin.
Kadafur ya kuma nuna rashin jin dadin yadda wasu masallatai suka bijire wa doka, inda a kullum sai sun kira sallah sai biyar, kuma sai sun yi jam’in sallolin sau biyar.
“Wasu masallatan ma ba su ko kashe lasifikar su. Haka su ke rika kwartsa kiran sallah da karfi, kowa na ji. To da haka Boko Haram ya fara.”
‘Coronavirus Sabuwar Fitinar Boko Haram Ce’:
Mataimakin Gwamnan Barno ya bayyana Coronavirus da cewa wata sabuwar fitina ce ta Boko Haram a jihar.
Ya ce lokacin da Boko Haram suka bullo, jama’a sun kauda kai daga ganin laifin su, har sai da abin ya yi muni tukunna.
“Duk wanda zai yi wasa da rayuwar sa, ya je ya yi ta yi, amma dai ni a matsayin mu na shugabanni, ba zan daina fada muku gaskiya cewa Coronavirus gaskiya ce, akwai ta.
“Ba zan daina Jan hankalin ku ku daina shiga cinkoson jama’a ba. Ku rika yin tsabta, ku killace kan ku ba, kuma idan za ku fita, to ku rika sa takunkumin rufe baki da hanci.”
Ya kara gargadin jama’a cewa su sani fa Coronavirus har yanzu ba ta da magani, said kame-kame kawai da ake yi.
Ya ce mutane 11 da cutar ta kashe a Barno, dama su na da kwantaccen ciwon tari, hawan jini da ciwon suga da kuma wasu cututtukan da ke tare da su.