Gwamnatin Jihar Jigawa ta bada sanarwar mutuwar mutum na biyu da cutar Coronavirus ta kashe a Jigawa.
Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar, kuma Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus na jihar, Abba Zakari, ya bayyana haka ga gidan Radiyon Freedom cikin daren Lahadi.
Zakari ya ce a wannan karo na biyu mace ce ciwon ya kashe a Karamar Hukumar Miga.
Ya ce a baya an kwantar da matar a asibitoci biyu, kafin daga baya aka yi mata gwaji, aka tabbatar da cutar Coronavirus tare da ita.
Zakari ya ce matar ta dauki cutar daga wurin mijin ta wanda ya dawo daga Lagos dauke da cutar.
Ya kara da cewa kuma ta na fama da wani ciwon ne kafin ma Coronavirus ta kama ta.
Kwamishina Zakari ya ce a yanzu haka jihar ta hana wasu almajirai har 950 zirga-zirga, a Kazaure, daga cikin garuruwan jihar da shi ma a cikin watan Afrilu aka killace shi saboda Coronavirus.
Sannan kuma ya ce an kwashi samfurin jinin mutum 679 an tura wata cibiyar gwaji mai zaman kan ta da Hukumar NCDC ta amince wa jihar da sahihancin sakamakon gwajin su.
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Gwamnatin Jigawa ta bada sanarwar mutuwar mutum na farko da cutar Coronavirus ta kashe.
Mutumin wanda ya dawo daga Legas dauke da cutar, dan asalun kauyen Fanisau ne cikin Dutse, babban birnin jihar.
Ya rasu ba da dadewa ba bayan an kai shi dakin killace masu fama da cutar Coronavirus a jihar Jigawa.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa bayan mutumin ya dawo daga Lagos ne ya fara rashin lafiyar da aka rika yi masa magani tare da shan magunguna, amma ciwo ya ki ci, ya ki cinyewa.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Jigawa Abba Zakari ya tabbatar da mutuwar mai dauke da cutar, kuma ya ce tun bayan samun labarin ba shi da lafiya ne aka gaggauta zuwa aka sinadaran jikin sa domin a auna shi.
Sai bayan da sakamako ya tabbata cewa ya na fama da cutar Coronavirus ce aka gaggauta daukar sa aka killace shi, inda ba da dadewa ba ya rasu.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa a yanzu akwai bullar cutar a Kananan Hukumomi 9 na Jigawa, wadanda ya ce tuni an rufe su, an hana karakaina.
Kananan Hukumomin sun hada da Gumel, Auyo, Gwaram, Kazaure, Miga, Taura, Birnin Kudu da Dutse.
Jihar Jigawa ta fara samun bullar cutar Coronavirus tashin farko lokacin da Jihar Kano ta dauki wani mai cutar dan asalin Jigawa ta maida shi can daga Kano.
Hakan ta sa Gwamnatin Tarayya sanarwar cewa an hana jihohi daukar mai dauke da cutar a maida shi wata jiha.
Ta ce duk cikin jihar da mai ciwo ya ke, to a can ne za a killace shi har ya warke.