An cafke maza 11 da ake zargi da yin lalata da ‘yar shekara 12 a Jigawa

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mazaje 11 da ake zargin sun rika afka wa wata ‘yar shekara 11 a kauyen Ma’ai suna yin lalata da ita.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Audu Jinjiri ya shaida cewa an damke wadannan mutane ne bayan kama mutum na 12 a daidai yana kokarin waske wa da wannan yarinyar wani lungu domin yin lalata da ita.

” ‘Yan sanda sun kawo mana wani mutum mai shekaru 57 da suka cafke a daidai ya na kokarin waske wa da wata yarin ‘yar shekara 12 wani lungu domin yin lalata da ita a kasuwar Limawa.

” Bayan an damke wannan mutum sai muka zurfafaf bincike, daga nan sai ya fallasa cewa ba shi kadai bane ya ke yin lalata da wannan yarinya, ya zayyano sunayen abokan sa da suka dade suna yin lalata da wannan yarinya akai-akai, da hakan ya kara masa kwarin guiwar shima ya aikata hakan.

Jinjiri ya ce tuni dai har an taso kewayar wadannan mutane an Kai su kotu domin ci gaba da bincike da yin Shari a Kai sannan kuma a yanke musu hukunci.

Share.

game da Author