Bayan watanni biyu a garkame, masallata sun yi Sallar Asuba a masallacin Al’Aqsa

0

Akalla masallata 700 ne suka halarci Sallar asubar ranar Lahadi a masallacin Baitul- Mukaddas da ke Kasar Israela.

Idan ba a manta ba, mahukuntan Kasar Israela sun rufe masallacin tun bayan bayyanar annobar Korona a kasar fiye da watanni biyu da suka gabata.

A yayin da ake bude masallacin an hori mutane da su yiwo alwalarsu daga gida, sannan kowa ya zo masallaci da dardumar sa.

Bayan haka an umarci kowa ya bada neasan akalla taku uku ko fiye a tsakanin sa na kusa da shi.

Haka kuma, masallacin annabi, dake Madina an bude shi domin masallata. Kamar masallacin Al-Aqsa, za a rika zuwa da darduma daga gida sannan da yin alwala daga can gida.

Kuma za a rika saka takunkumin fuska a duk lokacin da za a zo masallaci.

Share.

game da Author