Fitacciyar malamar koyar da darussan kasuwanci, kwalliya da dinke-dinken zamani a yanar gizo, Aisha Falke ta maida wa wandanda suke kushe gasar yi wa miji rangwada da ta saka ayi martani tana mai cewa ita ba ta ga illar abinda ma’auratan suka yi ba.
A wani bidiyo da ta saka a shafinta ta Instagram @aisha_falke ta bayyana cewa bata shirya yin haka don tozarta musulunci ko al’adun Hausa ba.
Sannan kuma ta ce ita ba yanzu take saka gasa irin haka ba, ” Na Kan sa a rubuta wa miji wasika a aji, kuma wata ta rubuta ta kuma fadi yadda mijin ta ya yaba.”
Falke ta ce ba ita ce ta fara saka bidiyon a yanar gizo ba, wata ce ta saka tana wa mijin ta rawa sai ita ma ta ga ya burgeta sannan ta ayyana yin gasar.
Ta ce ko da ta saka bidiyo na farko, wasu sun yi mata caa akai sai ta sauke bidiyon duk da ta saka cewa za ta ba wanda tafi iya yi wa mijinta rangwada kudi naira 20,000 sannan kuma ta Kai ta gidan abinci na kasaita a Abuja su ci abincin rana ko na dare.
Sannan kuma ta ce Wanda ya saka cewa wani ya saki matar sa, ba haka bane bayan bincike da tayi ta gano cewa ya shirga karya ne.
A karshe ta ba ‘yan Arewa shawarar cewa akwai abubuwa da dama da ya kamata a maida hankali akai wajen hana faruwarsa kamar fyade da ake yi wa yara kanana da dai sauran su.
Saidai kuma malama Aisha bata ji da dadi ba daga malamai da wasu ‘yan Arewa da ke ganin wannan gasa bai dace ta saka shi ba ko kuma ta ingiza mutane su yi ba.
Malamai sun kushe wannan abu da kakkausar murya, suna masu cewa ba tarbiyar addinin musulunci bane mace ta rika rangwada a gaban mijinta ta sannan ta saka a yanar gizo kowa ya ga yadda take jujjuyawa tana girgiza jiki.
Ita dai Aisha Falke ta ce bata ga illar haka ba domin ita ma ta yi wa mijinta amma bata dauka ta saka a yanar gizo wa duniya kowa ya gani ba.