Yadda harkokin noma suka bunkasa tattalin arzikin Najeriya tsakanin Janairu zuwa Maris, 2020 -NBS

0

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana yadda harkokin noma suka kasa samun karsashi da tagomashin bunkasa tattalin arzikin cikin gida na Najeriya a cikin watanni ukun farko na shekarar 2020.

Kididdigar ta bayyana dalla-dallar yadda harkokin noma da suka hada da noman amfanin gona, kiwon dabbobi, bunkasa gandun dazuka da kuma kiwon kifi suka bunkasa tattalin arziki a wadannan watanni uku na farkon 2020, fiye da farkon watanni ukun shekarun 2019 da na 2018.

NBS ta fitar da wannan jadawalin kididdigar bayanan tattalin arzikin cikin gida, wato GDP a ranar Talata.

Lissafi tiryan-tiryan ya nuna cewa an yi hada-hadar tattalin arzikin cikin gida har ta naira tiriliyan 16.7 tsakanin Janairu zuwa Maris, 2020.

A cikin wadannan adadin kudade, an yi hada-hadar naira tiriliyan 3.7 kacokan a bangaren sabatta-juyar-tar kayan amfanin gona.

Hakan ya na nufin kashi 21.96 na bunkasar tattalin arzikin cikin gida (GDP) din ya samu ne daga harkokin noma.

GDP dai na nufin adadin bunkasar tattalin arzikin cikin kasa, daga hada-hadar kayyakin duk da ake samarwa a cikin kasar da sauran ayyuka ko duk wata cinikayya da hada-hadar kudade a cikin kasa.

Hakan ya na nufin ba a lisaafawa da hada-hadar safarar kayyakin da aka shigo da su daga kasashen waje. Haka ma babu lissafin hada-hadar da Najeriya ta yi a kasashen waje, kamar sayar da danyen man fetur, da sauran su.

A shekarar 2019, harkar noma ta bayar da gudummawar kashi 20.89, kuma a shekarar 2018 dai noma ya bayar da gudummawar bunkasa har ta kashi 20.66.

Nazarin da NBS ya yi, ya nuna cewa ba don cutar Coronavirus ta barke tun a cikin watan Fabrairu ka’in da na’in ba, to da gudummawar bunkasar da harkar noma zai bayar a farkon 2020 cikin watanni ukun, za ta zarce ta kashi 21.96 da ya bayar.

Nazarin duk da annobar Coronavirus, ya nuna cewa noma ya bunkasa tattalin arzikin kasa da kashi 2.20, idan aka kwatanta da farkon watannin 2019.

Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata, Shugaban Kasa muhammadu Buhari ya na kunnen ‘yan Najeriya cewa su kara tashi tsaye wajen noma abinci.

Buhari ya ce a yanzu Najeriya ba ta da sukunin wadatar kudaden da za a rika amfani da su, ana sayo kayan abinci daga kasashen waje.

Share.

game da Author