Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabbin mambobin kwamitin gudanarwar Kamfanin Mai ta Kasa, NNPC.
A sanarwan haka wadda maitaimaka wa shugaban kasa Kan harkokin yada Labarai, Femi Adeshina ya fitar ranar Asabar, Buhari ya nada mambobin kwamitin gudanarwar Kamfanin Mai daga yankuna shida na kasarnan.
Wadanda aka nada sun hada da, Mohammed Lawal (Arewa Maso Yamma), Tajudeen Umar (ArewaMaso Gabas), Adamu Mahmood Attah (Arewa Ta Tsakiya), Senator Magnus Abe (Kudu Maso Gudu), Dr Stephen Dike (Kudu Maso Yamma), da Chief Pius Akinyelure (Kudu Maso Yamma).
Dukkan su za su yi aiki na tsawon shekara uku ne.
Discussion about this post