Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabin sa karo na uku a kan Coronavirus a yau Litinin, karfe 8 na dare.
A daren na yau ne wa’adin dokar zaman gida na kwanaki 14 da aka kakaba wa Abuja, Lagos da Ogun ke cika.
Wa’adin na kwanaki 14 shi ne karo na biyu, domin kwanaki 28 kenan jihohin biyu da Abuja su na kulle.
An kulle sun ne tun lokacin da masu cutar Coronavirus ba su wuce 77 a Najeriya ba. Amma ya zuwa Lahadi da dare akwai mutum 1,273 da aka tabbatar da kamuwar su. An sallami mutum 239 kuma 40 sun mutu.
Cikin wadanda suka mutu har da tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.
Yayin da ake kara ko ci gaba da kulle wasu jihohin, ana sa ran Buhari zai kara wa’adin ne, duk kuwa da cewa akwai gwamnonin da ke so a sassauta dokar.
Ranar Lahadi kuma Buhari ya gana da Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire da Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa, Chikwe Ihekweazu a kan batun dokar hana fita da kuma rahotannin yawan mace-macen da ake samu a Kano.
Kwanaki biyar kenan aikin gwajin Coronavirus ya tsaya cak a Kano.