Najeriya na cikin matsancin fama da karancin kayan gwajin masu dauke da cutar Coronavirus.
Shugaban Hukumar Kula da Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja. Da ya ke karin bayani a shafin sa ba Twitter, Ihekweazu ya ce akwai matukar karancin kayan gwaji, wadanda ya ce ana bukatar karin masu yawan gaske domin a yawaita gwajin da ake yi a kowace rana a kasar nan baki daya.
Shugaban na NCDC ya kuma yi bayani dalla-dalla na irin kayayyakin gwajin da Najeriya ke bukata, sunayen su da kuma sunayen kamfanoni da masana’antun da ke yin su.
“Kayan gwajin da Najeriya ke bukata ruwa a jallo a halin yanzu su ne samfurin RNA wanda aka yi a kamfanin Qiagen ko na ThermoFischer, ko na SeeGene, ko na Inqaba ko na kamfanin LifeRiver da sauran su.”
Wannan bayani na Shugaban NCDC ya zo daidai lokacin da ake korafin cewa Najeriya ba ta tabuka abin kirki idan aka yi la’akari da yawan wadanda ta yi wa gwaji a kasar nan.
Kasashe da yawa wadanda ba su kai yawa da karfin Najeriya ba, irin su Ghana da Afrika ta Kudu, sum yi wa mutane da dama fiye da Najeriya gwaji.
Sama da mutum 1000 suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya zuwa ranar Jama’a da ts gabata.
Najeriya ce koma bayan yawan wadanda aka yi wa gwaji a cikin kasashen da sama da mutum 1,000 suka kamu da Coronavirus.
Ranar 1 Ga Afrilu Najeriya ta ce za ta kara yawan mutanen da ts ke yi wa hwajo a kullum daga 500 zuwa 1,500.
Ranar Alhamis da ta gabata Najeriya ta ce za ts fara yi wa mutum 4,000 a kullum gwaji, inda a kullum za a yi wa mutum 2,000 gwaji a Lagos, sauran jihohi kuma mutum 2,000.
Sai dai kuma Kungiyar NIDS ta ce wannan magana duk tatsuniya ce, domin har zuwa yau mutanen da Najeriya ta yi wa gwaji kadan suka haura 10,000.
“In da a CE a kullum Najeriya na yi wa mutum 1,500 gwaji, kun ha ai a cikin sari uku za a iya yi wa mutum 30,000 gwaji kenan.” Cewar kungiyar.
Discussion about this post