Kungiyar Kare Hakkin Musulmai karkashin jagorancin Ishaq Akintola, MURIC, ta gargadi gwamnan jihar Anambara Obiano da ya shigar taitayinsa ya daina nuna son Kai da wariya a jihar sa.
Akintola ya kalubalanci wannan Gwamna da ya koma ya sake jawabin sa da yayi sannan ya nuna kowa nashi ne ba kawai sai kai kirista bane.
Gwamna Obiano na Jihar Anambara ya sassauta dokar hana walwala inda ya ya ce gidajen giya da shakatawa za su iya budewa da wasu wuraren sana’a. Sannan kuma ya ce Kiristoci za su iya bude wuraren ibadar su wato Coci-coci amma bai ambaci musulmai ba.
” Ko su musulmai ba mutane bane da zai rika sassauta dokokin jihar yana ambatan kungiyoyin banda na musulunci.
” Ina so in tuna mishi cewa akwai musulmai ‘yan Arewa da ke zaune a jihar sannan akwai dubban ‘yan asalin jihar da musulmai ne, amma bai ambato su ya ce ga yadda za su rika Yi ba. Kawai ya maida su saniyar ware a jihar.
” Yau da ace Shugaba Buhari ne ko wani gwamnan Arewa yayi irin wannan jawabin, ya ambaci musulunci bai ambato Kiritoci ba da kowa yaji hayagagar su ta ko-ina suna korafi su an nuna musu bambamci, su ana ci musu fuska a kasar nan don kiristoci ne su.
A dalilin haka, Akintola yayi kira cikin gaggawa, Obiano ya koma ya sake maida jawabin sa. Ya ambaci kowa da kowa banda nuna wariyar jinsi ko addini.