Sama da mutum milyan 135 na fuskantar matsalar abinci a duniya – Rahoto

0

Sama da mutum milyan 135 a kasashe 55 suka afka cikin hatsarin matsalar abinci a duniya, kamar yadda Rahoton Karancin Abinci Na Duniya na 2019 ya tabbatar.

Wannan rahoto ya ce matsalar za ta fi muni a cikin wannan shekara ta 2020, saboda fantsamar Coronavirus a duniya. Sai dai kuma rahoton bai bayyana irin tsananin da yunwar za ta yi mummunar illa ba.

Rahoton wanda shi ne na 4, ya ce ba a taba samun irin wannan tsananin rashin abincin ga dimbin mutane masu yawan gaske a duniya ba, kamar a wannan shekara.

Har ila yau, rahoton ya ce cikin shekarar 2016, yunwa ta nukurkusar da mutum milyan 108 a kasashe 48. Cikin 2017 kuma yunwa ta kassara mutum milyan 124 a kasashe 51. Cikin shekarar 2018 kuwa, mutum milyan 118 yunwa ta dawwara a cikin kasashe 53.

Mutum milyan 73 daga cikin milyan 135 da yunwa ta sabauta cikin 2019, du a kasashen Afrika su ke, kuma rabin su a cikin kasashe 36 daga cikin kasashe 55 na Afrika.

Rahoton ya kara wata fatawar cewa mutum milyan 5 daga cikin su, a Arewacin Najeriya yunwa ta bi su ta yi musu fyadar-‘ya’yan kadanya.

Yemen da Congo da Afghanistan ne yunwa ta fi kassarawa, inda Yemen da Congo kowace na da sama da mutum milyan 15 da yunwa ta kwantar, yayin da Afghanistan akwai sama da mutum milyan 11.

Rahoton ya rashin abinci ya na nufin rashin abinci mai gina jikin da dan Adam zai iya ci ya rayu.

Wannan rahoton ya kara da cewa matsalar za ta kara muni a wannan shekara a duniya, musamman saboda yadda cutar Coronavirus ta yi wa duniya mummunar illa, kuma ba a san rana ko lokacin fita daga wannan kangin annoba ba.

Share.

game da Author