Gwamnan Kaduna, Nasir EL-Rufai ya bayyana cewa daga rana irin ta yau, kowa zai fita daga gidan sa ko zuwa wajen aiki dole sai ya saka takunkumin fuska.
El-Rufai ya kara da cewa gwamnati za ta wadata marasa karfi da miskinai.
El-Rufai ya gode wa mutanen Kaduna sannan kuma ya ce a ci gaba da nesa-nesa da juna.
” Bayan fama da cutar da nayi, ko makiyi na bana mai fatan ya kamu da wannan cuta. Saboda haka kowa ya yi taka tsantsan da wannan cuta kuma a kiyaye da cudanya cikin mutane fiye da mutum 10.
Idan ba a manta ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya warke daga cutar coronavirus da yayi fama da ita har na tsawon makonni hudu.
El-Rufai ya bayyana cewa anyi masa gwaji sau biyu, kuma sakamakon ya nuna bashi dauke da cutar.
Sannan kuma ya godewa mataimakiyar gwamnan jihar Hadiza Balarabe bisa ayyukan da ta rika yi lokacin da yake killace.
Idan ba a manta ba El-Rufai ya bayyana kamuwa da wannan cuta ranar 28 ga watan Maris.
Haka ita ma uwargidan gwamna El-Rufai, Hadiza El-Rufai, bayyana jin dadinta bisa ga sakamakon gwajin gwamna sa da ya nuna ya warke daga cutar.
Bayan haka, Kwamishina Lafiya na jihar Kaduna Amina Balona ta bayyana cewa an sallami mutum daya da ya warke daga Coronavirus a jihar, sai dai kash an samu karin mutum uku da suka kamu a jihar,
Daya daga ciki wani matashi ne da ya dawo daga Kasar Turkiyya, sai kuma wasu mazaje biyu da suka yi dakon cutar daga jihar Kano.
A karshe ta yi kira ga mutane su kaurace wa yawan yin tafiye-Tafiye musamman zuwa jihohin da cutar ta yi tsanani.
Discussion about this post