CORONAVIRUS: Za a iya yada cutar coronavirus ta hanyar yin numfashi

0

Sakamakon binciken da cibiyar ‘United States’ National Academy of Sciences (NAS)’ ta yi ya nuna cewa za a iya yada cutar ta hanyar numfashi. Cewa mutumin da ya kamu da cutar zai iya yada ta ta iska.

Sannan za a iya kamuwa da cutar ta hanyar rashin tsaftace hannu, yawan taba fuska, baki, ido da hanci.

Bisa ga wannan bayanai ya zama dole mutane su rika saka takunkimin fuska idan za a fita domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Cibiyar NAS ta kuma ce akwai yiwuwar cewa kwayoyin cutar za su iya makalewa a jikin kayan da aka sa na kariya a lokacin aiki.

Haka na nufin cewa mutum zai iya kamuwa da coronavirus idan ya taba wadannan kaya da aka yi amfani da su.

Haka kuma masu sharan dakin da ake kwantar da marasa lafiya na iya dauko kwayoyin cutar a jikinsu duk wanda ya taba su na iya kamuwa da cutar.

Sai dai kuma har yanzu hukumar lafiya ta duniya WHO na nan a kan bakanta na cewa mutane za su iya kamuwa da Wannan cuta idan aka Yawaita kusantar wanda ke dauke da cutar.

A yanzu haka mutane 1,004,458 ne ke dauke da cutar sannan sama da 50,000 sun mutu a duniya.

A Najeriya mutane 210 ne suka kamu da cutar, daga ciki 20 sun warke sannan 4 sun mutu.

Share.

game da Author