COVID19: Kalubalen da ke Yankin Arewacin Najeriya, Daga Khadijah Sulaiman

0

A hankali a hankali cutar coronavirus naci gaba da yaduwa a Najeriya.

Duk da irin gargadi da matakai da ake dauka a jihohi daban-daban, tsoro saikaruwa yakeyi a zukatan jama’a.

A yanzu haka dai 000 akwai kididdiga ta Jami’ar John Hopkins da ke nuni dacewa kimanin mutane 538,000 ne cutar ta kama a duniya, inda mutane 152,000suka sami lafiya, Sannan 34,000 suka rasa rayukansu.

A kasar Najeriya kuwa kididdiga da hukumar NCDC ke fitarwa a kullum ya nuna cewa akwai mutane 111 da suka kamu, inda mutane 3 suka warke, mutum1 kuma ya rasu. kididdigar ya nuna cewa jihar legas ce ke duke da masu cutarda yawa,sai Jihar Kaduna wacce take da mafi karancin mai cutar guda 1 watogwamna El- Rufa’i.

Jihar Kaduna dai itace jihar da tafi kowacce himma wajen daukar matakan kariya inda tuni tasa ka dokar hana fita ga jama’a.

Sai kwamtsam aka jigwamnan ya fito ya na nuni da cewa sakamakon gwajin da akamai ya nunacewa yana dauke da cutar, duk da bai nuna alamu ba. Sai dai a lokacin da cutar ke ta hankoron shigowa Arewacin Najeriya ta hanyoyi da dama, yankin na fama da wasu kalubale wadanda matukar ba’a kamo bakin zaren ba, tabbas cutar zata watsu fiye da yadda ba’a zato. Wadannan kalubale sun hada da:

1. Rashin bin doka da gwamnatin tare da hukumomin kare lafiya ke badawadon kare kai daga wannan cutar, da suka hada da nisantar taruka, wanke hannu da sauransu.

2. Rashi ko karanci kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da zasu yi gwajinwannan cuta.

3. Rashin cibiyoyin gwaji a Arewa, kayan aiki, ciki harda akwatin kayan gwaji, tufafin kariya ga malaman asibiti da sauran muhimman kayan aiki.A duk fadin Arewa wurin gwajin cutar Covid-19 guda daya ne wato a Abuja, inda kudanci ke da cibiyoyin guda 5,da karin wani a jihar Ebonyi.

4. A satin da ya gabata,munga kaya da fitaccen dan kasuwar China kuma shugaban kampanin Alibaba Jack Ma ya ba kasasshen Afirika ciki har da Najeriya. Najeriya ta amsa kayan na ta a ranar laraban makon jiya inda suka hada da abin rufe fuska 100,000,tufafin kare jiki 1000 da kuma akwatunan kayan gwaji guda 20,00 har yanzu bamu yadda za rabaw adanan kaya zuwa dukkanin jihohi ba.

5. Talauci da Jahilcin Wanda shi yafi cutar da Arewa a mafi yawan lokuta. akwai kaso na wasu mutane da basu yadda da wannan cutar ba. Acewar su duka lokacin da Allah ya rubuta zasu mutu, zasu mutu. Sunmanta da Karin magana hausawa da ke cewa:

‘Rigakafi yafi Magana’ dakuma ‘Taya Allah kiwo yafi Allah na nan’!A wani bangaren kuma Talauci na sa wasu cewa gwamnati ba ta basuabincin ci ba, ba yadda zasu yi su bi umurnin zama agida, ga iyali.Mafita ga Wadannan kalubale sun hada da:

1) Rage radaden yunwa da al’umma ke fama dashi tun kafin mazuwan wannan cuta, bare yanzu da ake ta sa dokar hana fita.

2) Ci gaba da wayar ma al’umma kai ga me da illar wannan cuta dakuma muhimmancin daukan matakan kariya. Amfani da hanyoyinmabanbanta wurin isar da sakon da suka hada da: malaman addini, Sarakuna, ‘yan siyasar, majigi, hoto mai motsi, rediyo, wasannin kwaikwayo, wake-wake na fadakarwa da sauransu.

3) Ingantan aikin malaman lafiya da basu kwarin guiwa yadda yakamata.

4) Gaggauta kara cibiyoyin gwaji zuwa dukkanin jihohi da kuma raba wadanan kayan da Najeriya ta samu kyauta, hadi da kudade ga dukkanin jihohi don fara gwaje-gwaje ma mutanen su.

5) Sannan, kamar yadda jama’a ke ta kira, ya kamata kowacce jiha taware asibitoci da zasu zama na gwaji don al’umma su samu wuringwaji kusa da su, ganin cewa cutar tana iya zama a cikin mutum batare da ta nuna alamu ba, kamar yadda muka gani a lamarin
Gwamna El-Rufa’i.

Wata majiya mai karfi na cewa akwai wasu jihohi da ke da kayan gwajin amma NCDC taki basu izinin fara aiki.

Yayin da na leka shafin hukumar NCDC na ranar 29/03/2020, ta wallafa cewar zatakara yawan cibiyoyin zuwa goma sha uku(13),nan da sati 3.

Dawannan Arewa zata sami jimillan cibiyoyi guda 5 akaduna,Maiduguri,Sokoto,Kano da Abuja.

Muna dai jiran nan da sati ukun, in cutar zata jira! Muna fatan ayiyadda akace din cikin kankannin lokaci a karshen, muddin gwamnoni da gwamnatin Tarayya tayi biris wurin shawo kan wadannnan da ma wasu kalubale, toh tabbas za’aiya shiga halin tasko.

Allah tsare mu

Khadijah Sulaiman.Malama a tsangayar koyar da aikin Jarida a kwalejin kimiyya da fasaha dakezariya.Khadijahsulaiman93@gmail.com

Share.

game da Author