Yadda na warke daga cutar coronavirus cikin sati daya – Gwamnan Oyo, Makinde

0

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya bayyana yadda ya kamu da cutar coronavirus sannan a cikin Sati daya ya warke gadagau.

Gwamna Makinde ya bayyana cewa tun bayan gwajin jininsa da aka yi a makon da ya gabata, kuma aka tabbatar masa cewa ya kamu da cutar coronavirus ya killace kan sa.

Ya ce Amala ya rika dirka sannan kuma yana kwankwadan Habbatussauda, Zuma da tsotsar Vitamin C a kullum.

” Tun da na shiga dakin da na killace kaina babu abin da na ke ci in banda Amala da nake narka, sai kuma hadin Habbatussauda da Zuma da nake Sha da maganin vitamin c.

” Haka na rika yi kullum har aka zo aka sake yi mini gwaji har sau biyu aka gano cutar ta Kama gabanta. Bata kwata-kwata a jiki na kuma.

Makinde ya ce don mutum ya kamu da Coronavirus kada ya dauka shikenan, akwai maganin da zai iya warkar da shi.
Za a iya warke wa kamar yadda nima na warke.

A karshe ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da taimakawa marasa galihu da talakawan jihar.

Yanzu gwamnonin Kaduna Nasir El-Rufai da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed da Suma sun kamu da cutar suka rage su fito daga asibiti.

Mutum 238 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, mutum sama da 30 sun warke har an sallame su kuma mutum 5 sun mutu.

Share.

game da Author