CORONAVIRUS: Mutane 23 sun kamu a Najeriya, yanzu 174

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta sanar cewa an samu karin mutum 23 da suka kamu da cutar coronavirus a sakamakon gwajin da ya fito ranar Laraba.

Adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya haura daga 151 zuwa 174 a kasar nan.

Wadanda suka kamu sun fito daga jihohin Legas dake da mutum 9, 7 a Abuja, 5 a jihar Akwa Ibom, daya a Bauchi sannan daya a Kaduna.

Jimlar wadanda suka kamu a Najeriya sun kai mutum 174 Sannan mutum 9 sun warke, 2 sun rasu.

Lagos- 91
FCT- 35
Osun- 14
Oyo- 8
Ogun- 4
Edo- 4
Kaduna- 4
Bauchi- 3
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-1
Benue- 1
Akwa Ibom- 5

Shugaban Hukumar NCDC ya bayyana cewa an kafa sabbin wauraren gwajin cutar a wurare da dama a kasar nan. Saboda haka za arika samun mutane da dama da za ayi wa gwaji yanzu.

Sannan kuma yanzu ana bi gida gida ne domin duba yan uwan wadanda suka kamu ko kuma suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.

Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.

Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukuma majalisan tarayya duk sun bada gudunmawar su domin taiamakawa hukumar NCDC kan aikin da take yi.

Share.

game da Author