CORONAVIRUS: Jawabin Buhari cike ya ke da dirkaniya -Inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta nuna damuwa dangane da yadda Shugaba Muhammadu Buhari bai tabo batun abin da ya fi damun ‘yan Najeriya ba, a jawabin sa dangane da annobar Coronavirus.

Jam’iyyar mai adawa, wadda a baya ta shafe shekaru 16 ta na mulkin Najeriya, ta ce babu komai cikin jawabin Buhari sai dirkaniya kawai, domin bai kamo hanyar magancewa da shawo kan manyan matsalolin da za su biyo bayan kafa dokar killace jama’a a gida ba.

A cikin jawabin, Buhari ya roki ‘yan Najeriya cewa su bada hadin kai da goyon bayan .dukkan matakan da Gwamnati za ta dauka, domin hana cutar Coronavirus fantsama a fadin kasar nan.

A martanin da ta fitar bayan jawabin na Shugaban Kasa, Kakakin PDP na kasa, KolaOlovbondiyan, ya ya ce: “Idan banda cewa da Buhari kowa ya kaurace wa shiga gungun jama’, sannan kowa ya killace kan sa a gida, to Buhari bai fadi wani sabon sabon abu ba.”

Ko su din ma tuni run kafin Buhari ya yi bayani kowa ya killace kansa a gida.

“PDP na cike da bacin rai cewa Buhari bai yi magana a kan abin da ya fi damun jama’a ba, musamman a garuruwan da ya kakaba wa mazauna jihohin da ya kakaba wa dokar hana fita a jihohi uku.

“Tir da yadda jawabin Buhari ya kasa tabo bukatun magunguna, hanyoyin saukaka wa al’umma kuncin rayuna nakai tsaye, ya kasa rage haraji da sauran su kamar rage kudin man fetur.

PDP ta nuna rashin jin dadin yadda Buhari ya kasa gabatar da talladin kai tsaye, sai ya buge da umarnin dakatar da biyan bashi tsawon watanni uku.

“Ya kamata Buhari ya gane cewa tun bayan bullar Coronavirus jama’a sun fidda barun ci gaba da biyan lamuni. Saboda haka, don ka ce su dakatar da biya sai nan da watanni uku, ai ba wata bajinta ce ka yi ba.”

Daga nan sai PDP ta ce ‘yan Najeriya sun zauna zaman jiran bayani daga shugaban su tsawon lokaci. Amma abin haushi, bayan an daukj lokaci mai tsawo, Buhari ya fito ya yi jawabin da babu komai da jama’a za su iya gadara da shi.

Jam’iyyar ta shawarci Buhari ya koma gida, ya zauna ya yi nazarin abubuwa masu muhimmancin da suka kamata ya yi wa jama’a a wannan mawuyacin halin barkewar cutar Coronavirus a nan Najeriya da duniya baki daya.

Share.

game da Author