CORONAVIRUS: A dakatar karbar kudin aikin hajjin bana a kasashe zuwa wani lokaci- Mahukunta kasar Saudi

0

Ma’aikatar kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar saudiyya ta yi kira ga kasashen duniya da su dakatar da karbar kudaden aikin hajjin bana daga jama’a zuwa aga yadda al’amurra za su kasance game da wannan annoba ta coronavirus.

A sako da ministan ma’aikatar aikin hajji da Umrah ya wallafa a shafinsa na Tiwita, minista ya ce mahukunta sun yanki wannan hukunci ne a dalilin barkewar cutar coronaviorus da ya karade duniya. Suna masu cewa dole sai an dan dakata tukunna zuwa aga abin da hali zai yi.

Bayan haka kuma ma’aikatar ta ce Saudiyya ta mayar wa da duk wanda da ya biya kudin bizar Umran na bana zuwa kasar. Sannan kuma duk mutanen da suka makale a Makka sakamakon dokar garkame kasashensu za su ci gaba zama a kasar kuma za a basu kyakkyawar kulawa har zuwa lokacin da kasashen su za su bude filayen jiragen su su amaido su gida.

Kasar Saudiyya na daga cikin kasashen da suke fama da cutar coronavirus. Duk da dai suna ta kokarin ganin cutar bai karade kasar ba gwamnati bata dauki abin da wasa ba tun a farko.

An rufe masallatan kasar banda masallacin harami da na madina domin gudun kada cutar ya kai ga wadannan garuruwa.

Bayan Haka an rage yawan mutanen dake dawafi a dakin a makka zuwa kalilan domin dakile yaduwar cutar.

Share.

game da Author