Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar na killace mutanen da ake zaton sun kamu da cutar coronavirus a wani Otel a Kano.
Ya ce an killace wadannan mutane bayan an dauki jinin su domin yi musu gwajin cutar kuna za su ci gaba da zama a wannan Otel har sai sakamakon gwajin nasu ya fito.
Ganduje ya fadi haka ne a lokacin da yake karbar bakonci shugaban Hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu da ya ziyarci jihar ranar Talata.
Ya ce duk mutanen da ake zaton sun kamu da cutar na zama ne a cikin gari da hakan ke nuna cewa cutar bata kai ga shiga kauyuka ba.
A dalilin haka ya sa gwamnati ke kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar a jihar.
Ganduje ya yi kira ga hukumar NCDC da ta taimaka wa jihar wajen kara yawan wuraren yin gwajin cutar.
Yadda Coronavirus ta yadu a jihar
Ganduje ya ce yawa da irin yanayin rayuwar mutanen jihar Kano ya sa cutar ke neman samun gindin zama a jihar.
A yanzu mutum 59 ke dauke da cutar a jihar wadda a dalilin haka ya jihar ta zama na uku a jerin jihohin da suka fi fama da cutar a kasar nan.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce Hukumar za ta tallafa wa jihar wajen yaki da cutar.
Ya ce NCDC ta ziyarci jihar ne domin ganin matakan hana yaduwar cutar da gwamnati ta dauka.
A yanzu dai mutane 665 ne ke dauke da cutar, 188 sun warke sannan 22 sun mutu.
Idan ba a manta ba, ranar Talata na makon jiya ne gwamna jihar Kano Abdullahi Ganduje ya saka dokar zaman gida dole a jihar.
Ganduje ya ce dokar zai fara aiki ne ranar Alhamis daga karfe 10 na dare kuma na tsawon kwanaki 7.
Ya umarci Jami’an tsoro za su hukunta duk wanda aka kama ya karya wannan doka da gwamnati ta saka.
Kafin cutar ta bullo a jihar gwamnati ta toshe duk iyakokin shiga jihar a matsayin matakan hana shigowa da coronavirus jihar.