Tun bayan barkewar annobar Coronavirus a duniya cikin watan Disamba, kasashen duniya suka rika killace garuruwa da kasashe, ta hanyar hana zirga-zirga.
Sai dai wannan duk bai hana mutane sama da 150,000 mutuwa cikin wadannan watanni ba. Haka kuma sama da mutum milyan biyu suka kamu da cutar a duniya.
A Najeriya, biranen Jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayya, FCT, Abuja aka fara kullewa, domin hana cutar yaduwa. Sai dai wannan duk bai hana ya zuwa ranar Talata sama da mutum 600 kamuwa ba, yayin da sama da mutum 20 cutar ta kashe.
Me ya sa dokar hana fita ba ta hana kamuwa da cutar Coronavirus ne?
1. Bonono, rufe-kofa-da-barawo: Dukkan garuruwan da ake hana shiga ko karakaina, ba a rufe su kafin cutar ta shiga ba, sai bayan ta bayanna a jikin wani.
Wannan ne ke sawa bayan an rufe sai a ci gaba da samun bullar cutar a cikin al’ummar garin, ko da kuwa wani bako bai sake shiga da ita ba.
2. Bayyana wa’adin ranar kulle gari: Wannan ma wata babbar rashin dabara ce, kuma sagegeduwa ce. Idan aka bayyana cewa za a rufe gari nan da kwana biyu, ba a san yawan masu cutar da ke yin hijira daga wani gari su shiga garin ba kafin a kulle.
Sannan kuma duk wanda ba ya son a kulle shi a cikin garin, idan ya na da cutar, zai iya ficewa dauke da ita, ya kai ta wani gari.
3. Ware wasu ranakun shiga kasuwanni: Wannan ma ya na maida hannun agogo baya, domin a duk ranakun da ake bude kasuwannin jama’a na haduwa a gwamutsu da juna. Wanda ba shi dauke da cutar, zai iya dauko ta a kasuwa ba tare da ya san a wurin wanda ya dauki cutar ba.
Jama’a da dama na alakanta yawaitar masu cutar Coronavirus a Kano da irin cinkoson da ya faru a kasuwannin garin, a daren jajibirin kulle Kano. Mutane sun cika kasuwanni domin kokarin sayen kayan abinci, saboda hana karakainar da za ta fara aiki washegari.
4. Raba Tallafi Ko Raba Coronavirus?: Hukumar Kula Da Cututtuka ta Kasa ta hana gwamutsuwar jama’a da taron cinkoso, domin kauce wa kamuwa da Coronavirus. Amma abin takaici jami’an Ma’aikatar Bayar Da Agaji, Jinkai Da Inganta Rayuwar Al’umma na tara daruruwa da dubban mutane, su na kokawar karbar kudi ko kayan tallafi.
Yadda ake kokawa, banke-banke da gugumarar karbar kudade da kayan agaji, kai ka ce an fito da tsarin ne domin a watsa cutar Coronavirus a cikin talakawa.
5. Rashin Bin Doka Da Kin Daukar Matakan Kariya: Babban gari kamar Kano da aka hana harkoki, hakan bai hana jama’a ci gaba da haduwa wuri daya ba.
Manya ba su zaman gida, sai zaman majalisa a kofar gida. Yara da matasa kuwa sai wasannin kwallo suke yi.
6. An Ki Sharar Masallaci Ana Share Kasuwa: Gwamnati ta hana jama’a shiga masallatai su yi sallah, gudun kada cinkoso ya sa jama’a su kamu da cutar Coronavirus.
Amma abin mamaki, matasa sai tikar wasannin kwallo su ke yi cike da filayen kwallo, jar a cikin unguwanni, amma jami’an tsaro na gani.
Irin yadda dandazon ‘yan kallo ke zuwa kashe-kwarkwatar, za a iya baza cutar Coronavirus a filayen, daga can a yi dakon ya zuwa cikin gidaje.
7.Rayuwar Kunci Da Talauci: Akasarin mazauna birane talakawa ne fitik, wadanda ba su da sukuni a cikin gidajen da suke haya, ballantana har su sakata su wala, su ji dadin zaman gida.
Yanayin gidajen dama, gidajen kwana ne kadai, amma ba gidajen zama ba ne. Magidanci ba ya iua zama gidan. Shi ya sa ko da yaushe ya na kofar gida zaune, an kafa majalisa. Da dare ya shiga ya kwanta. Da safe kuma ya jefo kafar sa waje, ya fice.
8. Matsalar Ruwa da Wutar Lantarki: Babu jiha ko garin da zai yi tutiyar cewa a Najeriya ba su fama da matsalar ruwa da ta hasken lantarki. Wannan ma matsaloli ne da ke hana talaka iya zaman killace kan sa a gida.
9. Jahiltar Annobar Coronavirus: Da yawan mutane ba su yarda da cutar ba kwata-kwata. Wasu kuma na ganin cewa akwai ta, amma addu’a ce kadai maganin ta, ba wai killace kai, ko hana cakuduwa a masallaci ba. Wasu kuma sun yarda akwai ta. Amma babu ruwan su da daukar matakai. Wato dai su a wurin su, kushewar badi sai badi.
10. Rashin Daukar Gwamnati Da Muhimmanci: An zo lokacin da talakawa sun fara raina duk wani bayani ko wayar da kai da gamnati za ta yi musu. Ko dai saboda yadda su ke ganin wasu da murdiya ko da jagaliyanci suka hau mulki da tsiya, ko kuma yadda su ke ganin cewa manyan kasar nan da suka ki gyara kasa, su ne suka fita waje suka fara jajibo cutar Coronavirus suka dawo da ita. Shi kuma talakan da ke zaune a gida, an kulle masa kan iyaka, abincin da ya ke dan samu a cikin rahusa, yanzu ya na neman ya gagare shi.
To wane kurari ko barazana ce kuma za a yi masa da cutar Coronavirus?