CORONAVIRUS: Mahaifiyar kociyan Man City, Guardiola ta rasu a Barcelona

0

Mahaifiyar kociyan kungiyar kwallon kafan Manchester City Pep Guardiola, Dolors Sala Carrio mai shekara 82 ta mutu a a garin Barcelona Bayan fama da ta yi da cutar coronavirus.

Jama’a sun yi tururuwa wajen aikawa da sakon ta’aziyyar su ga tsohon dan wasan Barcelona din kuma kociyan Manchester City.

Kasar Spain na daga cikin kasashe uku da cutar coronavirus ta yi wa matukar illar gaske. A cikin mako guda ta rasa dubban mutane a sanaiyyar kamuwa da cutar.

A ranar Litinin kawai mutum 637 suka mutu a kasar. Yanzu haka an tabbatar da mutuwan mutum sama da 13,000 a kasar.

Mahaifiyar Pep na zauna ne a garin Barcelona, garin da cutar ta fi yaduwa cikin garuruwan kasar Spain.

A ranar Lahadi, tsohon dan wasan Barcelona, Xavi da matarsa suka tallafa wa asibitin Barcelona da gudunmawar Ero Miliyan daya.

Haka a wasu Kasashe, Ana samun irin wannan tallafi daga attajira da manyan ma’aikatan gwamnati.

Yanzu dai an dakatar da wasannin kwallon kafa a fadin duniya a dalilin barkewar annobar coronavirus.

Share.

game da Author