A daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya ta rufta cikin mummunan halin da ba ta taba ruftawa ba gwamnatocin ba. Kuma a daidai lokacin da katutun bashi ya yi wa Najeriya yawa, sai kuma ga shi za ta sake kinkimo wani bashin har na naira tiriliyan 3.2, domin yi wa cutar Coronavirus kwaf-daya.
Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, ranar Litinin a Abuja, lokacin da ta ke bude asusun neman lamunin naira bilyan 500 da za a fara fafata yaki da cutar Coronavirus.
Ta ce Najeriya ta fara tsara yadda za a ciwo bashin har na naira tiriliyan 3.2 domin gagarimin aikin kakkabe cutar Coronavirus a kasar nan.
Zainab ta bayyana yadda za a ciwo bashin, inda ta ce mafi yawan kudaden za su fito ne daga Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Bankin Duniya da kuma Bankin Bunkasa Kasashen Afrika.
“Za mu karbo bashin dala bilyan 7.05(kwatankwacin naira tiriliyan 2.68) a kan farashin kowace dala kan naira 380.
“Wadannan kudaden za a yi amfani da su wajen Inganta wannan shirin yaki da Coronavirus na naira bilyan 500.
“Tuni har mun cika fam na neman a ba mu bashin gaggawa na naira dals bilyan 3.4 daga Bankin Bada Lamunina Duniya domin mu yi wa Coronavirus kwaf-daya da kudaden.
” Dama kuma IMF ta amince kasa za taiya neman lamunin da bai wuce adadin karo-karon kudaden da ta ke zubawa a asusun ba.
” Shi ya sa mu ka nemi a ba mu na adadin kudaden da Najeriya ta Zuba baki daya.
” Shi wanann bashi ba a gindaya wa kowace kasa wasu sharuddan karbar sa ba. Kuma a yanzu kasshe 80 ne suka nemi a ba su bashin domin yaki da Coronavirus.”
Zainab ta ce kudaden da Bankin Bada Lamuni (IMF) zai bayar, su ne za su samu da wuri, nan da makonni shida.
Bashin Bankin Duniya kuwa da na Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, sai nan da wattani biyu ko uku za mu fara tunanin samun kudaden.
A cikin kudsden dai Zainab ta ce za a yi kokarin an aamar wa matasa aiki akalla mutum 1,000 cikin kowace karamar hukuma 774 da ake da su a Najeriya.
Discussion about this post