NUNA FIFIKO: An ba jihar Legas naira biliyan 10 na coronavirus, mu ba a bamu ba – Gwamnan Ribas

0

Gwamnan jihar Legas, Nyesom Wike ya kalubalanci gwamnatin tarayya, cewa shugaban Kasa Buhari ya ba jihar kudin coronvirus kamar yadda ya ba jihar Legas tallafin naira biliyan 10.

Akwai akalla mutum 234 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Jihar Legas na da 120, Ribas na da mutum daya.

Gwamna Wike ya soki kokarin gwamnatin Buhari na yaki da cutar coronavirus da take yi, yana mai cewa Buhari ya maida abin siyasa, da hakan ke neman ya jefa Najeriya cikin halin kakanikayi idan ba a mai da hankali ba.

Jihar Legas ce cibiyar Kasuwancin Najeriya, amma kuma Ribas ita ce arzikin man kasar nan ke kwance. jihar ta fi kowacce jiha samar wa Najeriya da kudaden shiga. Saboda haka dole ita ma a bata wani kason kudin coronavirus.

” Ban ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya ta tsame jiha daya tal ba. Ko tana nufin sai an samu akalla mutane 50 ne sun kamu da cutar za a ba jiha tallafi daga gwamnatin tarayya. Dukkan mu jihohin kasa daya ne, saboda haka kada a nuna fifiko akan wata jiha.

A karshe ya bayyana cewa maralafiya daya da a ka samu ya na dauke da cutar coronavirus a jihar ya soma samun sauki. Sannan kuma za a ba mutane dama su fita su garzaya kasuwa domin siyan kayan abincin bukin Easter ranar Talata da Laraba.

Share.

game da Author