Yadda cutar coronavirus ta kawo mana cikas a haska wasanni da kallo a Najeriya

0

Mutane da dama sun fi gane wa garzayawa gidajen haska wasannin kwallon kafa domin kallo a Najeriya. Wannan karshen mako ya zo wa masu irin wannan gidaje cikas a dalilin dakatar da duk wasannin da ake bugawa a nahiyar Turai.

Cutar coronavirus ta tada wa mutanen duniya hankali da dama sannan tayi sanadiyyar dakatar da duk wasanni a nahiyar Turai. Hakan yasa hatta masu amfana da wadannan wasanni, wato gidajen haska wasanni sun fada cikin halin ha’ula’i na rashin kudi.

PREMIUM TIMES ta zazzagaya wurare da dama da ake haska wasanni a Kaduna kuma sun iske su duk a kulle.

Wasu daga ciki da aka tattauna da masu gidajen sun bayyana cewa ba su ji dadin hakan ba.

” Mu dai rokon mu shine Allah ya kawo karshen wannan annoba a duniya. Amma ko a lokacin da ake hutun wasanni ba a samu matsalar ace wai kwata-kwata babu wasan da za anuna a gidan kwallo ba. Wannan annoba ya sa kusan komai ya tsaya cak. babu abin yi kwata-kwata. Hatta ‘yan kallo ma basu ji dadi ba.

” Mu wannan shine sana’ar mu kuma da shi muke al’amurorin mu. Wasu da dama suna da abin kallon a gidajen su amma kuma sun fi kaunar su garzayo nan su kalla saboda yakan yi musu kamar suna can ne.” Inji Mani Wani mai gidan kallo a Kaduna.

Unguwannin da wakilin mu ya zazzagaya, kamar su Barnawa, Tudun Wada, Narayi, Badikko, Badarawa duk zancen dai daya ne.

Steven Sani da shima yana da irin wannan gidan kallo a Narayi Kaduna ya ce, haka dai za su zuba Ido su ci gaba da addua’ domin ba su ba ma kasuwanci a duniya kaf ya tsaya.

” Irin mu da sana’ar mu kenan dole muji ba dadi domin, sai mu haska muke samu miya ta yi ja. Ka ga ko wannan annoba da ya karade duniya bai yi mana dadi ba a harkokin mu. Muna rokon Allah ya kawo mana karshen sa mu samu komai ya dawo daidai.

Yanzu dai kusan dukkawasanni a duniya an dakatar da su zuwa wani lokaci tukunna a samu a iya shawo kan wannan annoba. Sai dai kasuwanci da cinikayya yana samun matsalar gaske a dalilin yaduwar cutar.

Dubban mutane ne a duniya suka kamu da cutar sannan wasu da dama sun rigamu gidan gaskiya a kasashe sama da 100 da cutar ta bayyana a ciki har da Najeriya.

Allah Ya kawo mana sauki ya kiyaye, Amin.

Share.

game da Author