Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga baki dake zama a kasar da su kwantar da hankalinsu duk da cewa an samu wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya cewa kada su kidime.
Ministan kiwon lafiya Osagie Ehnaire ya bayyana haka a hedikwatar Ma’aikatar aiyukkan waje dake Abuja yana mai cewa bai kamata a tsorata mutane ba game da cutar.
Ranar 27 ga watan Fabrairu wani dan kasar Italiya dauke da cutar ya shigo Najeriya ta tashar jiragen sama dake Legas inda bayan ya sauka ya wuce zuwa jihar Ondo.
Ya ce an killace wannan mutum a asibiti a Legas a lokacin da aka gano ya kamu da cutar sannan ma’aikatan kiwon lafiya suka gudanar da bincike domin gano mutanen da suka kamu da cutar a dalilin mu’amula da shi.
Ehnaire yace an gano mutum daya da ya kamu da cutar a jihar Ondo a dalilin wannan binciken inda aka hada wannan mutum da dan kasar Italiya aka killace su domin kula da su.
Ya ce za a sallame su da zaran sun samu sauki.
Bayan haka Ehaire ya kara da cewa gwamnati ta karfafa matakan hana yaduwar cutar Coronavirus a kasar ta hanyar kafa wuraren yin gwajin cutar a tashoshin jiragen sama da ruwa sannan ta zuba kayan gwajin cutar a sashen yin gwaji dake manya –manyan asibitocin gwamnati a kasar nan.
Ehnaire ya ce duk da cewa gwamnati bata hana shige da fice ba zuwa kasashen waje daga kasar nan mutane su guji zuwa kasashen da wannan cuta ta yi wa hawan kawara kamar su Chana, Iran, Italiya, Korea ta Kudu da Japan.
Ya kuma yi kira ga hukumomin jiragen sama a kasashen waje da su rika yi wa mutane gwajin cutar kafin jiragen su tashi cewa rashin yin haka ne ke yada cutar zuwa kasashen duniya.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa mutane sama da 100 sun kamu da coronavirus a kasashen Afrika 11.