A wannan lokaci da ake fama da rudanin coronavirus a duniya, a Jihar Taraba ranar Juma’a mahara suka arce da Ango da abokan sa 6 a daidai hanyarsu ta dawowa daga bukin aure a garin Gboko jihar Benuwai.
Maharan sun tare motan dake dauke da Angon da Abokanan sa a daidai Titin Wukari-Ibi.
Wani shugaban al’umma ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa maharan dukkan su fulani ne. Sun tare motan angwayen sannan suka arce da su.
” Muna fama da hare-haren ‘Yan bindiga a wannan hanya. Abin yayi mana yawa yanzu. Amma kuma duk mun san su kuma muna neman hadin kan jami’an tsaro ne domin mu dagargazasu.
” A gaskiya dole mu yaba wa jami’an tsaron yankin domin suna taimakawa.
Maharan sun buka ci a biya naira miliyan 10 kafin su saki angwayen, sai dai mutanen gari sun ce ba za su biya su ba domin ma sun san su.