COVID-19: GARKAME TALAKAWA: Akwai Bukatar Gwamnati Da Attajirai Su Taimakawa Talakawa, daga Mustapha Soron Dinki

0

Cewa mutane su zauna a gida babban abu ne a gwamnatance, wannan shi ake kira da turanci “tough decision of government”. Tabbas yana da wahala gwamnati ta yanke irin wannan doka, amma idan irin wannan annobar tazo dole za a iya zartar da hakan.

Da wahala amma ya zama dole. Bamu da zabi, ga gidaje irin namu a kuntace, kuma wutar lantarki tafi karfin talakan Najeriya.

A fannin tattalin arziki kuwa, musamman a kasashe irin namu yana da matikar wahala ka kulle mutane a gida, saboda mutane suna rayuwa ne irin ta tsuntsu. Ma’ana, kullum sai sun fita suke samun abinda zasu ci.

Irin wadannan mutanen suna rayuwa ne hannu-baka-hannu-kwarya. Wasu ma daga cikinsu, awoyi ashirin da hudu (24 hours) na kowacce rana sun yi musu kadan saboda bugabuga.

Wannan karatu ne wanda talakawa ne ‘yan uwana kawai zasu iya ganeshi. Muna kira ga gwamnati da attajirai masu karfi da su taimakawa mutane bayan sun bi umarnin zama a gida. Gaskiya naji dadi da naga gwamnoni sun jajirce wurjanjan wajen yaki da coronavirus.

Allah ya kara dafa mana, bayan haka zamu so muga an tallafawa talaka da abinci da wutar lantarki saboda zaman gidan yayi masa dadi.

Gaskiya haka muka ga kasashe suna yi, tallafin gwamnati daban, tallafin attajiran kasar daban. Kuma su attajiran ba gwamnati suke bawa kudin ba saidai idan da wata manifar, gidauniya suke yi su rabar wa da talakawa abinci ko kudi.

Wannan shi ake kira da “qarfi da qarfe”. Gashi nan yana faruwa a Iran, Italy, Spain, Ingila da Chana. Gidauniyar taimako iri-iri daga attajirai. Ko tamu gwamnatin ta shiryawa hakan kuwa? Allah ya basu ikon taimakawa.

Bayan haka, ayi kokari kada siyasa ta shigo cikin harkar bayar da tallafin, saboda tudun-mun-tsira muke nema yanzu ba siyasa ba. Rigimar duniya inji Bahaushe da mai rai ake yin ta. Allah ya bamu wucewa lafiya kafin zuwan watan azumin Ramadan. Don Allah, talakawa su bi umarnin gwamnati su koma gidajensu, komai lokaci ne.

Allah ya kawo mana karshen annobar cikin ikonsa.

Share.

game da Author