Da Sunan Allah, Mai Rahamah, Mai Jinkai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta, Annabin karshe, Muhammad Dan Abdullahi, da alayensa da sahabban da dukkanin wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Allah madaukakin Sarki ya fada a cikin Alkur’ani mai girma cewa:
“…Sun dauki malamansu da masu ibadarsu da Isa Dan Maryama abun bautawa suka bar Allah, alhali an umurce su ne da su bautawa Allah shi kadai…” [Suratut-Taubah, 31]
A wannan ayar, Allah Ta’ala ya bamu labari cewa yahudawa da nasara sun mayar da malaman su da masu Ibadar su abun bautawa suka bar Allah. Bautar Isa Dan Maryama a wurin nasara abu ne sananne da baya bukatar dogon sharhi. To amma ta yaya ne mutane zasu mayar da malamansu abun bautawa su bar Allah mahaliccin su? Annabi (SAW) ya bamu labarin yadda mutane suke butawa malamansu su bar Allah, a cikin ingantaccen Hadisin da Imamu Tirmizi ya ruwaito. Annabi (SAW) yace:
“…Bautar ita ce, malamansu suna basu fatawa (akan kuskuren fahimta) kuma su bi su akan haka. Duk abun da malaman suka halatta masu koda haram ne to zasu dauke shi a matsayin halal. Haka duk abun da suka haramta masu koda halal ne to zasu dauke shi a matsayin haram (ma’ana suna yiwa malaman makauniyar biyayya, ido rufe)…”
Anan Annabi (SAW) yana nufin sun dauki malaman nasu tamkar Allah, ta hanyar bin fatawowin su ido rufe, ko da kuwa fatawar ba daidai bace. Suna yi masu makauniyar biyayya, marar kaidi. Duk abun da malaman suka fada, kawai su a wurin su haka yake, zasu bi, babu kuskure, kuma ko da ya sabawa Shari’ah. Sannan wani lokaci ma suna kallon malaman na su kamar ma’asumai, wadanda basu yin kuskure. Sanadiyyar haka ne, ya zamanto duk wanda yayi kasadar nuna kuskuren malamin su, to ya shiga uku.
Wannan ya nuna kenan mutum ya karbi fatawar wani malami ido rufe, wata hanya ce da zata iya kai mutum ga shirka. Don haka wajibi ne a gare mu mu kiyaye, duk malamin da yayi fatawa mu tambaye shi dalili da hujja daga Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW), da kuma fassarar magabata da suka gabace shi a wannan fahimta ta shi. Yin haka zai taimaka muna wurin kaucewa afkawa cikin rudani, hadari, fitina da shirka. Maganar Allah da Manzonsa da ijma’i ko haduwar malamai shine hujja ba ra’ayin kowane malami ba shi kadai, musamman ma idan ra’ayin nasa baya kan hanya. Don haka ta’assubanci da wani malami, kuma ko wane malami ne, wannan ya sabawa Shari’ah, kuma baya halatta. Musamman a cikin irin wannan yanayi da muka samu kan mu a ciki na kowa malam ne.
Sannan a fahimce ni, ba wai ina cewa ne kar abi malamai ba, a’a, abun da nike cewa shine, kar mu bi malamai ido rufe, kar ya kasance muna yiwa malamai makauniyar biyayya, ta yadda duk abun da suka kwaso zamu bi shi a haka, mu yarda da shi, kuma ko da a cikin abun nan akwai halaka babba.
Duk malaman nan guda hudu, Iimaman Musulunci, wato Abu Hanifah, Malik, Shafi’i, Ahmad Ibn Hanbali, da ake danganta mazhabobin nan hudu zuwa ga re su, sunyi kokarin kiran al’ummah da gargadin su cewa kar wanda ya yarda ya bi su ido rufe, sun sanar da dalibansu cewa, kar wanda yayi masu makauniyar biyayya wadda Shari’ah bata yarda da ita ba. Amma mu ayau, zaka ga wasu malaman ma sune suke kiran mabiyansu da suyi masu irin wannan makauniyar biyayya, kuma sun san bai dace ba, saboda rashin tsoron Allah.
Ga duk mutumin da ke bibiyar kafafen yada labarai na zamani, da sauran kafafe, yasan da cewa kwanan nan wasu abubuwa na bacin rai da bakin ciki da damuwa sun faru a cikin wannan al’ummah tamu ta Najeriya, kuma suna cikin faruwa, sanadiyyar makauniyar biyayyar da muke yiwa wasu malaman addini, da kuma ta’assubancin da muke yiwa wadansu shugabanni da kungiyoyin addini.
Sanadiyyar annobar Korona bairos (Coronavirus) ko kobid naintin (Covid-19) da Allah Madaukaki ya jarabi duniya baki daya da ita, wadda ta zamanto mai hadari ga rayuwar bil adama da kuma tattalin arzikin duniya. Gwamnatoci da jami’an lafiya da malamai da jagororin addini na kasashe daban-daban na duniya, sun ga dacewar a dauki wasu matakai masu muhimmanci, da zasu taimaka wurin takaita yaduwar wannan annoba mai hadari da kuma dakushe kaifin ta, saboda shawarwari da masana a fagen kiwon lafiya suka bayar. Daga cikin shawarwarin da suka bayar, akwai cewa ya kamata mutane su kaucewa haduwa wuri guda, ko a cunkushe wuri guda, da kowace irin manufa ce, domin wannan suka ce yana daga cikin matakan da kasar China suka dauka, inda wannan annoba ta samo asali, suka ci nasarar takaita yaduwar ta, domin cuta ce mai saurin yaduwa cikin sauri.
Wannan al’amari yasa shugabanni a duniya, da jami’an lafiya da jagororin addini na kowane kasashe suka dauki irin wadannan matakai. Najeriya ma ba’a bar ta a baya ba wurin daukar irin wadannan matakai. Shugabanni sunyi kokari, kuma ma suna kan yi, haka jami’an lafiyar mu Allah ya sani, suna iya kokarin su, haka ma malaman mu da jagororin addinin mu sun yi kokari, kuma sunyi abun da ya dace. Tun daga majalisar koli mai kula da harkokin addinin Musulunci a Najeriya, har zuwa Jama’atu Nasril Islam, duk karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, har zuwa limamai da malamai, duk duniya ta shaida sun yi kokari, kuma sunyi abun da ya dace. To sai dai amma kash… An samu wasu malaman da sam basu fahimci inda aka sa gaba ba. Domin sun bijire, sun ki yin biyayya ga shugabanni da jami’an lafiya, kuma sun ki su hada kai da sauran malamai ‘yan uwan su domin a hada hannu wurin ganin an yaki wannan annoba cikin taimakon Allah. Bana zargin wadannan malamai da jahilci, a’a, ko kadan. Sannan ba zan iya cewa sun bi son zuciya ba, a’a, amma dai ina iya cewa a gaskiya wannan fahimta tasu, da wannan fatawa tasu kuskure ce da zata iya jefa al’ummar Musulmi cikin fitina, da rudani, da tashin hankali mai girma!
Aukuwar annoba a tarihin Musulunci da kuma koyarwar addinin Musulunci akan yadda Musulmi zasu yi idan Allah ya jarabe su da aukuwar annoba, har zuwa matakan kariya da rufe masallatai, da kauracewa taron jama’ah, da kebe marasa lafiya, duk abu ne da Musulunci yayi cikakken bayani, kuma malamai sun yi bayanai cikakku akai, sun fadakar da al’ummah, kuma sunyi kokari sosai, wanda duk wanda yake mai adalci, babu abun da zai yi illa ya yaba masu, amma ba sai na sake maimaita bayanan su anan ba.
Amma dai abun da zan ce anan shine, a gaskiya maganganun da babban Malamin mu, Dr. Ahmad BUK yayi game da wannan matsalar annoba, da matakin rufe masallatai, da shi da ire-iren sa, kamar su Sheikh Bello Yabo Sokoto, Sheikh Umar Sani Fagge, ba daidai bane. Fatawar da Sheikh Abdulrazak Yahaya Haifang ya bayar ba daidai bace, (Amma maganar da yayi cewa bidi’ah ne ayi Sallah a wawware haka ne, kai duk wanda yayi haka ma bashi da Sallah). Sannan maganganun da Alhaji Sani Yahaya Jingir yayi da kuma bijirewa shugabanni da yayi, ya jagoranci Sallar juma’ah a Jos, shima ba daidai bane. Domin tafarkin amintattun Malamai ya yarda da barin Sallar jam’i a Masallaci, da rufe Masallatan domin wata larura ko tsoro ko gudun wani hatsari da zai fadawa al’ummah. Jama’ah kuyi Sallolin ku a cikin gidaje, ku roki Allah a duk inda kuke, lallai Allah mai ji ne, kuma mai tausaya wa bayin sa ne. Ba daidai bane wasu su tafi suna cewa wai ana so a rusa Masallatai ne, ko kuma ana so ne a hana Musulmi yin Sallah. Duk wannan bai dace ya fito daga bakin Malamai ba. Kuma ba daidai bane da wasu ke cewa wai ana bin yahudawa da Amerika ne. Kuma mu sani, al’ummar Musulmi ba da fuskantarwar yahudawa ko Amerika suke ganin halaccin rufe Masallatai don larura ba, a’a da tafarkin amintattun Malamai ne suke ganin wannan halacci. Kuma duk wanda yace ku kangare wa hukuma da jami’an tsaron ta, ku sani ba tafarkin amintattun Malamai yabi ba, a’a tafarkin son ransa ne yabi. Kuma ku sani irin wadannan masu kiran kuyi tawaye, wallahi babu wanda yafi su raki, kuma babu wanda ya kai su tsoro idan fitina ta barke ko annoba ta barke. Kune zaku raunata, kuma masifar zata kare a kan ku ne ku mabiya, amma su ‘ya’yansu mafi yawanci suna can a killace, imma dai suna karatu a kasashen waje, ko kuma wasunsu ma ‘yan rayuwa ne, suna bin rayuwar turawa, amma iyayensu a nan suna ta yi maku ihu da hargowar cewa ana kawo maku rayuwar turawa da akidun su don a hana ku addini. Ku sani, wallahi idan kunne yaji to gangar jiki ta tsira!
“ولا يطاع عالم في باطل، والحق مقبول وان من جاهل.”
Ma’ana:
“Ba’a yin makauniyar biyayya ga Malami idan ya kauce hanya,
Amma ita kuwa gaskiya za’a karbe ta koda kuwa jahili ne ya fade ta.”
Haka Abdullahin Gwandu ya fada Allah ya jikansa da rahama, kuma da ikon Allah muna akan wannan!
Kuma duk Malamin da ya bayar da fatawar da zata cutar da al’ummah, to ya sani alhaki yana kan sa!!!
Sannan ina ganin babu wanda zai yi musun cewa yiwa shugabanni tawaye da rashin girmama su, da rashin yi masu da’a da kallon su a matsayin basu isa ba, da kallon su akan masu kokarin halakar da al’ummar Musulmi, shine makasudin samuwar ‘yan ta’addar Boko Haram a kasar nan. Sannan jama’ah su fahimci cewa na buga misali ne kawai da wannan, amma ban ce Sheikh Jingir da mabiyansa ‘yan Boko Haram bane, amma ya kamata mu sani, irin wannan halin da yake nunawa, to komai yana iya faruwa! Sannan a kiyaye, babu inda nace hukumomi suyi wa Sheikh Jingir irin hukuncin da ake yiwa ‘yan ta’addar Boko Haram, amma dai mu sani, wallahi hanyar da ya dauka, hanya ce mai hadari sosai ga wannan al’ummah!
Kuma ina sane da cewa girmama malamai dole ne kuma wajibi ne a shari’ah. Ina ganin babu wani musulmi da bai san da haka ba. Amma kuma a daya gefen, ni ina da fahimtar cewa, babu da’a da biyayya da girmamawa ga duk mutumin da bai girmama dokokin Allah da Manzonsa da kuma maslahar al’ummah ba, kuma ko da malami ne shi! Domin duk wanda zai kalli dokokin Allah da manzon sa da rufin asirin da al’ummar Musulmi suke ciki, da zaman lafiyar su, yayi masu karan-tsaye, to wannan babu wani girma da ya cacanci ka bashi. Shin wai har kullun, me yasa ne ba zamu kalli rashin girmama Allah da Manzonsa da girmama shugabanni da girmama sauran malamai ‘yan uwansa, da girmama maslahar al’ummah da Sheikh Jingir baya yi ba? Nayi imani da Allah, babu wata kasa da ta san abunda take yi, da zata amince da irin wadannan dabi’u da halayen kangara da taurin kai na Sheikh Jingir. Misali, da a kasashen Amerika yake ko Saudi Arabia ko Egypt ko Morocco, ko Kuwait ko Malaysia da sauran su, wallahi da yanzu ya rasa ‘yancin sa na yin wa’azi gaba daya, wannan abun da kowa ya sani ne babu jayayya akai, sai dai fa idan in son zuciyar mu zamu bi.
‘Yan uwa, wallahi da zamu taimakawa kasar mu Najeriya, wurin zartar da hukuncin da ya dace akan ko wane mai laifi, kuma komai matsayinsa a cikin al’ummah, ba tare da nuna alfarma ko jin tausayi ko wani abu mai kama da haka ba, da kasar nan Allah ya tausaya muna, ya jikan mu, ya gyara muna ita cikin sauki! To amma mun kasance sai abu ya faru, ga gaskiya kiri-kiri muna gani, mun san ta, amma sai muyi kememe, mu tsaya muna wani lungu-lungu da kwana-kwana, saboda tsoron wani mutum ko wasu mutane.
Sannan don Allah meye matsayi da hukuncin mutumin da yake yin wasu ayukkan da zasu iya jefa al’ummah da kasa baki daya cikin bala’i? Me yasa wasu kasashe suka sanya dokar hukuncin kisa ga mutumin da yake shigar masu da kwayoyi cikin kasa? Kun ga ai sun sanya hukuncin ne saboda ganin cewa al’ummar ce baki daya yake neman ya halakar da kwayoyin nasa. Don haka suke ganin a kawar da shi shi kadai shi yafi da ace abar shi ya halakar da al’ummah baki daya.
A kasar nan, barin kowa yana fadar abun da yaga dama da sunan malanta ko da sunan wa’azi shine ya jefa mu cikin wannan hali da muka samu kan mu a ciki a yau. A yau akwai kasashen da duk ilimin ka, duk karatun ka, idan hukuma bata amince da kai ba, ko kuma aka fahimci a cikin wa’azin ka akwai alamomin tunzura jama’ah ko jefa al’ummah cikin halaka, ko hada husuma da gaba da kiyayya, to ba zaka yi wa’azin ba! Duk mun san da wannan! Amma a Najeriya ne kawai kowa yake da damar ya fadi abinda yake so, kuma komai munin sa, sai ya kai ga jawo muna bala’i sannan muyi ta shan wahala wurin kokarin shawo kan sa!
Don girman Allah mu binciki shafukan su Sheikh Jingir da magoya bayansa a Facebook da WhatsApp, mu ga yadda suka mayar da shi wani irin jarumi. Sannan kuma suna yada cewa wai duk wanda bai yi Sallar juma’ah ba a Najeriya to shi munafuki ne. Kuma wai su kadai ne Musulmin kwarai a Najeriya. Sannan a wani bidiyo, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nuna cewa duk Musulmin da suka biye wa yahudawa, suka ki yin Sallar juma’ah to sunyi riddah. Yanzu don Allah jama’ah ya kamata a kyale wannan ayi shiru, ko ayi saku-saku da lamarin sa? Yanzu don Allah meye wannan? Don Allah ba da haka ne su Muhammad Yusuf na Maiduguri suka fara ba? Wallahi mune ya kamata muce bamu yarda ba, sai anyi muna adalci, ba wani ne zai gaya muna wai muyi wa su Sheikh Jingir adalci ba. Domin shi babu wani rashin adalci da al’ummah tayi masa, amma shi ga rashin adalcin sa nan ga wannan al’ummah ya bayyana a fili karara.
Sannan kuma mu sani, duk malamin da ya janye wannan fatawar tasa da bata kan hanya, wato ya canza ra’ayinsa, ya yarda ya kasance tare da sauran malamai ‘yan uwan sa, to dole sai ya fito ya bayyanawa duniya sabon matsayinsa. Sai yayi jawabi a bidiyo, a yada wa al’ummah matsayinsa. Domin kamar yadda ya yada waccan fahimtar tasa ta farko, magoya bayansa suka yi aiki da ita, to sai ya yada canza ra’ayin da yayi domin duk wanda ya gani, ya dauki waccan fahimtar ta farko, shima ya canza ra’ayinsa, kuma a gyara barnar da wannan fatawar tayi.
Daga karshe ina son mu sani, wallahi babu wani Malami da baya da girma da matsayi a wurin mu, amma fa duk da haka, dokar Allah da Manzonsa da maslahar wannan al’ummah, sun fi muna kowane Malami. Babu inda akace kawai saboda mutum shi Malami ne, sai a bar shi yayi ta abunda ya ga dama! Kawai ayi ta bin sa ido rufe ana yi masa makauniyar biyayya. Sai ya kai al’ummah ya baro, ko ya kai ga jawo wa al’ummah bala’i sannan ace ai ba’a sani ba. A’a! Musulunci sam bai ce haka ba!
ina rokon Allah ya kawo muna mafita daga wadannan fitintinun zamani, amin.
Ya Allah, ina tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka. Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW). Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi daga wannan jarabawa ta annoba, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.