Coronavirus: Majalisar Kolin Musulunci ta bada umarnin rufe dukkan masallatan Abuja

0

Majalisar Kolin Musulunci a karkashin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ta bada umarnin a rufe dukkan masallatan da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Cikin wata takardar da Daraktan Gudanarwar Majalisar Koli, Yusuf Nwoha ya sa wa hannu, an umarci kowane Musulmi ya rika yin sallar sa a gida.

Dama kuma tun a safiyar Litinin din Kwamitin Babban Masallacin Juma’a na Kasa da ke Abuja, ya bada sanarwar kulle masallacin, domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Nwoha ya ce an cimma matsayar amincewa a rufe dukkan masallatan Abuja ne bayan an cimma yarjejeniya tsakanin Sultan Sa’ad da kuma manyan malaman Musulunci.

Sultan wanda shi ne Sarkin Musulmi, kuma shi ne Shugaban Majalisar Kolin Musulunci na Najeriya.

Sanarwar ta yi kira ga dukkan limaman masallatan su bi wannan umarnin da aka bayar na rufe masallatan, har zuwa lokacin da za a bada sanarwar sake bude su.

An kuma yi kira ga al’ummar Musulmi su bai wa gwamnatin tarayya hadin kai domin a gaggauta shawo kan cutar Coronavirus, kada ta yi mummunar barkewa a kasar nan.

Share.

game da Author