Yayin da masana kimiya ke gudanar da bincike domin samun kyakkawar fahimtar cutar Coronavirus kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mutane musamman masu shan taba ko masu shakar hayakin taba da su nisanta kansu da haka cewa busa taba da shakar hayakin ta na sa a gaggauta kamuwa da cutar.
WHO ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da masana kimiya suka gudanar a wuraren gwaji 55,2924 dake kasar Chana.
Sakamakon binciken ya nuna cewa dayawa daga cikin mutanen da corononavirus ta yi mummunar ko suka mutu na dauke da wasu cututtuka a jikinsu da suka hada da cututtukan dake kama zuciya, nunfashi, hawan jini, ciwon siga, daji, tarin fuka da makamantan su.
Sakamakon ya kuma kara nun cewa mutanen da suka kamu da irin wadannan cututtuka sun kamu da su ne a dalilin shan taba da suka yi a shekarun baya ko suke yi har yanzu.
Kungiyar kiwon lafiyar ta ce duk da cewa babu tabataccen sakamakon binciken da ya nuna cewa akwai alaka da shan taba da cutar Coronavirus amma kamata ya yi mutane su kiyaye domin guje wa kamuwa da cutar
CORONAVIRUS
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.
A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.
Cutar da ta samo asali a kasar Chana a watan Disemba 2019 ya kama mutane 80,849 sannan da dama sun mutu a kasar.
Coronavirus ta yaduwa zuwa wasu kasashen duniya inda mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.
A yanzu dai kasashen Italiya da Masar a Najiyar Afrika na cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya.