Yadda Boko Haram suka kashe Sojoji shida a Barno

0

Majiya mai karfi ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wasu mahara ‘Yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya guda shida a garin Banki dake Maiduguri jihar Barno.

Wadannan mahara sun kai wa sojojin harin bazata a daidai mahadar Banki inda suka buda musu wuta suka kashe shida daga cikin su.

Wani soja da baya so a fadi sunnan sa ya bayyana cewa wannan abin tashin hankali ya auku ne ranar Lahadi da safe a lokacin da maharan suka yi wa sojojin kwantar bauna suka bude musu wuta.

Wakilin PREMIUM TIMES ya tattauna da kakakin rundunar sojin Najeriya Sagir Musa inda ya bayyana masa cewa bashi da masaniyar haka ya faru a mahadar Banki da Maiduguri.

“A gaskiya ban san me ke faruwa game da abinda kake so in yi maka bayani a akai don bana Najeriya, Ina Landan yanzu haka.”

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Boko Haram suka kai hari a garin Dapchi, inda suka kashe wasu ’yan sanda 6.

Boko Haram sun kai harin a Dapchi, wani kauye cikin Jihar Yobe.

Hukumar bada agaji na jihar (SEMA) sun kasa tantance sauran gawarwakin farar hula biyu da aka kashe, ko su wane ne ba.

Tsakanin ‘yan sanda, sojoji ko bilitante babu wanda ya iya shaida ko jami’an su ne ragowar gawarwakin biyu ba.

Share.

game da Author