Coronavirus: Daraktan Kungiyar Gwamnonin Arewa ya killace kan sa saboda cudanya da Gwamnan Bauchi

0

Babban Daraktan Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Asisha Okauru, ya bayyana cewa shi da matar sa da sauran iyalan sa sun killace kan su, sakamakon cudanyar da ya yi da Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

An dai bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ya kamu da cutar Coronavirus bayan ya gaisa hannu da hannu da dan Atiku Abubakar, wanda shi ma aka gano ya kamu da cutar.

Cikin wata sanarwa da Okauru ya turo wa PREMIUM TIMES da jijjifin safiyar Laraba, ya ce ya yanke killace kan sa da iyalan.sa ne saboda ya cakudu a wurare da dama tare da Bala Mohammed.

Ya ce sun zauna wurin daya a taron gwamnoni na na Majalisar Tallalin Arziki da sauran su. Don haka ne ya yanke shawarar killace kan sa a gida.

Matar Okauru, mai suna Ifueko Omogui Okauru, ta taba rike mukamin Shugabar Kwamitin Hukumar Kula da Hukumar Tattara Kudaden Haraji. Yanzu kuma ta na jagorantar wata Gidauniyar Agazawa Dattawa ce mai suna DAGOMO.

Sanarwar ta ce tuni aka bada shawarar cewa dukkan ma’aikatan ofishin ta su killace kan su a gida.

Haka ma ma’aikatan ofishin Kungiyar Gwamnoni, su ma an ba su shawarar su ci gaba da yin aiki daga gida, ko kuma zaman gida din.

“Duk da dai a wurin tarukan da mu ka gudanar, wanda Gwamna Bala ya na ciki, duk an dauki kwararan matakai na kariya, duk da haka babu wani tabbacin sanin hakikanin al’amarin, tunda ba gwaji aka yi mana ba, ballantana a gane wanda ya kamu da wanda bai kamu ba. Shi ya sa ba killace kai na da iyali na.” Inji Okauru.

Share.

game da Author