CORONAVIRUS: Gwamnan Edo ya killace kan sa

0

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya killace kan sa tare da mika samfin din sinadaran jikin sa domin a yi gwaji, bayan yay i cudanya da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugagab Kasa, wadanda dukkan su sun kamu da cutar.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Lbarai na Obaseki mai suna Crusoe Osagie ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa gwamnan ya killace kan sa tare da tura sinadarai domin a yi masa gwaji a gano shi shi ma ya kamu ko bai kamu din ba.

Ya ce “Gwamna ya killace kan sa, bayan ya cakudu da Gwamna Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, wadanda su biyun an tabbatar da cutar Coronavirus a jikin su.

Ya ce Obaseki ya gana da Bala ne a wurin taron gwamnoni, sannan kuma ya gana da Abba Kyari.

Yayin da gwamnati ke ta kara sa himma wajen ganin ta zakulo wasu da ake tunanin sun kamu ko kuma sun cakuda da wadanda suka kamu, wasu manya na ci gaba da killace kan su da kan su.

Da safiyar Laraba din nan ne Babban Daraktan Kungiyar Gwmnonin Najeriya ya bada sanarwar killace kan sa da iyalan sa, bayan haduwar da ya yi da Gwamna Bala a wurin taron gwamnoni.

Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana killace kan sa, ta bakin kakakin sa, Laolu Akande, tun daga ranar Talata da dare.

Share.

game da Author