Akalla jihohi bakwai ne aka samu tabbacin yaduwar cutar coronavirus a kasar nan.
Coronavirus ta bullo a kasar nan ne bayan wani dan kasar italiya dake dauke da cutar ya shigo Najeriya.
Tun daga wannan lokaci cutar ta fara yaduwa a kasan.
Bisa ga sanarwar hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) mutane 46 ne ke dauke da cutar, biyu sun warke sannan daya ya mutu a kasar nan.
NCDC ta sanar da haka ne ranar Laraba bayan ta gano cutar a jikin mutane biyu daya a Abuja sannan daya a jihar Legas.
Hukumar ta ce 30 daga cikin mutanen da suka kamu da cutar na cikin wadanda suka shigo kasar nan daga kasashen waje a makon da ya gabata.
Jihar Legas ce jihar ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar inda a jihar mutane 30 na dauke da cutar.
Abuja mutum 8, Ogun mutum 1, Oyo daya, Ekiti daya, Edo daya, Bauchi daya, Osun daya.
A dalilin haka jami’an kiwon lafiya na gudanar da bincike domin gano mutanen da suka kamu da cutar ta hanyar cudanya da wadanda ke dauke da ita.
Bayan haka an kuma samu tabbacin cutar a jikin jami’an gwamnati biyu a kasar nan wato da Muhammed Bala gwamnan jihar Bauchi sannan da hugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari wanda duk suna killace.
Daga nan kuma Da safiyar Laraba Babban Daraktan Kungiyar Gwmnonin Najeriya ya bada sanarwar killace kan sa da iyalan sa, bayan haduwar da ya yi da Gwamna Bala a wurin taron gwamnoni.
Shi ma Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana killace kan sa
Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya killace kan sa sannan ya bada jininsa domin yin gwajin cutar.
Obaseki ya killace kan sa, bayan ya cakudu da Gwamna Bala Mohammed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye domin kare kai daga CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.