CORONAVIRUS: Buhari ya fusata da manyan da ke karyar sharuddan da Gwamnati ta gindiya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya soke taron shugabannin kasashen Yankin Tafkin Chadi saboda matsalar Coronavirus.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, inda ya kara jaddada kokarin da Najeriya ke yi wajen dakile cutar.

Ministan ya kara da cewa daga yanzu Buhari ya daina gaisawa da kowa a kasar nan, wato gaisuwar musabiha. Kuma ya ce har yanzu ‘yar sa ba can a killace.

Har ila yau an takaita masu kai ziyara a Fadar Shugaban Kasa, kuma an tilasta kowa ya rika wanke hannu sinadarin tsaftace hannaye.

Sannan kuma Buhari ya fusata da labarin yadda wasu manyan jami’an gwamnati ke bijire wa ka’idojin da gwamnati ta gindaya ta yin kaffa-kaffa da cutar Coronavirus.

Ya ce duk wanda aka kama ya na bijirewa, to doka za ta hukunta shi.

A wata sabuwa kuma, Minista Lai ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su saurari kafa tsauraran dokoki domin kariya daga Coronavirus.

Ya ce tabbas za a shiha mawuyacin hali nan gaba, amma wannan hanya ce ta shawl kan wannan cuta domin hana ta fantsama.

Share.

game da Author